‘Yan sanda a Amurka sun ce mutumin da ake
zargi da gwajin wani karamin jirgin sama mara matuki daya kade wata mata har ta fita
hayyacin ta, ya mika kansa ga hukuma. Jirgin ya bugi matar ne a kanta bayan ya rikito a
cikin wani gida.
Jami’ai na ci gaba da bincike dangane da lamarin, wanda ya auku ranar Lahadi.
Lamarin shi ne irin shi na baya bayan nan da wani
jirgin kai sakonni mara matuki ya raunata wani
mutun.
‘Yan sandan Seattle suka ce saurayin matar ne ya rike ta lokacin da jirgin ya bige ta, sannan daya daga cikin abokanenta ya mika wa ‘yan sanda
jirgin da hoton mutumin da suke gani shi yake
gwajin jirgin. Daga baya wani mutun ya tuntubi ‘yan sanda a
matsayin wanda ya ke da alhakin lamarin.