1⃣ kai tsaye ta shiga hall din batare
da shakkar malamin dake ajinba ko
kuma laakari da lattin datayiba,yanayi
n tfyrta cikin isa da qasaita shi ya
janyo hankalin mutanen dake hall din
tare da malamin xuwa gareta,bata
damu da kallon da malamin k mata
ba tacigaba da taunar cingam dinta
tana fitar da sauti,ta xare madubin
dake idanunta tana Neman gurin
xama da alama hall din acike yake
kasancewar malamin dake hall din
tsoronsa ake baya wasa ko kadan ya
dubi agogon hannunsa qarfe goma da
rabi saura minti biyar ya gama lecture
amma ihsan k shigo masa aji ynxu ya
dubi ynda aka xubo masu idanu
domin aga wane hukunci xai yanke
akanta amma ya kasa aiwatar da
komai domin yasan wacece ihsan....ta
juyo tana kallonsa tace malam ina
buqatar gurin xama ta fada a
yangance ya soma murmushi yace
ranki ya Dade ki tayarda Wanda
kikeso ki xauna,ta juya tana kallonsu
daya bayan daya ta tsaida idanuwanta
akan Bilal yaron dakeji da kansa
fagen kyau da kudi ta lura Sam ba
ruwansa da matan skul din sai baqar
taqama da qasaita tace Bilal gurinka
xakaban na xauna,kallonta yake cike
da mamaki yanda tasan sunansa
sannan ta rasa waxata tayar duk fadin
hall din sai shi yayi kwafa batare da
gardamaba ya tashi ta isa gurinda
yatashi cikin qasaita ta
xauna,malamin ya cigaba da lecture
dinsa.
Bayan gama lecture sunfito tare da
qawarta Rukayya ta jingina a motarta
tana kallon rukayya tace Ruky
yaushene birthday din naki batare
data kalletaba tace dadina dake
xumudi inkinji mgnr party kamar
xakije aljannah ,tayi tsaki bayan ta
yatsina fuskarta tace Ashe laifine Dan
na nuna xaquwata akanki mtsew
menene ma acikin partyn naki kudin
arxiki baki dashi danma xn
taimakamiki,tay i Jim tana tunanin
hali irin na ihsan komai sai tayima
gori akansa tace naji bnda kudin ai ba
matsalarki bane,ta kalleta tace ni
kawai Allah ya jarabceni da qawance
dake mtsew ta gyara tsayuwarta tace
duk da hakama inasonki shiyasa nake
jure wulakancinki adai dai lokacin da
Bilal ya iso gurin tare da safwan
fuskarsa cike da bacin rai ya nunata
da yatsa sai yau na tabbatar da
abinda ake fada kanki bakida mutunci
wannan yaxama karo na farko daxaki
hada kanki dani danni ba ajinkibace
tayi dariya sosai hrda taba hannunta
tace kaji matsalar talaka kome xanyi
dakai ni,a wulakance yake kallonta ya
dubi motar ta yace da wannan motar
xaki dubeni ki kirani talaka ki dubi
motata da taki ki tantace talaka
tsakanina dake ta dubi motar ta
yatsina fuska tace wayasani kota
aroce dama nasan irinku ya harxuqa
ya daga hannu xai mareta safwan ya
riqesa yace kabarta kada ka daketa
macece tace kabarshi ya dakan ya
jawa Kansas balai ta juya ta shige
motarta ta tada ta fice hade da watso
masu ruwan dake kwance a qasa duk
jikin Bilal ya lalace ,safwan da
Rukayya k tafaman bashi haquri hrya
shiga motarsa ya cire rigar da wando
ya cillosu waje ransa abace yaja motar
dagashi sai singlet da guntun wando.