(Labari Mai Firgitarwa)
••••••••••••••••••••••••
Mai bada labarin yake cewa........ Wata rana mun gama
sallar juma'a mana tare da malam da sauran Dalibai, bayan
jama'a sun watse, sai ga wasu mutane sun shigo cikin
masallacin a firgice suna cewa ina Malam!!!
ina Malam!!! suna zuwa wajen Malam sai suka ce ya malam
muna da wani Saurayi(Matashi) ya Rasu tunda safe, Amma
ko da muka Haka masa kabarinsa muka sashi a ciki sai ga
wani Katon MACIJI
ya fito daga cikin kabarin, nan take muka razana muka rasa
yadda zamu yi shine muka zo nan mu fada maka,
nan da nan sai Malamin ya mike muma muka mike muka
tafi makabartar tare da malam, Muna isa makabartar sai
muka leka cikin kabarin sai ga wani irin Katon Macijin aciki,
ya fasa kai bindinsa yana wajen kabarin idanuwansa ya
zarosu yana Kallon mutane.
Ganin haka Sai malamin yace kubarshi ku sake Haka wani
Ramin, sai ko muka tafi nesa da kabarin farko kusan mita 20
muka haka wani kabari muna gab da gamawa sai ga Macijin
yana fitowa daga cikin sabon kabarin!!!
Sai malamin yace kuje ku duba kabarin farkon,
koda muka duba sai muka ga ya tsaga kabarin ya biyo cikin
kasa har zuwa sabon kabarin!!!
Sai malamin yace Wallahi ko mun haka na uku to sai mun
ganshi aciki don haka bamu da wani dabara sai dai mu
fitarda macijin daga ramin.
Mai bada labarin yace, Sai muka dakko sanda muka cikin
dabara muka fitar da macijin daga cikin kabarin, nan take
sai gashinan ya dawo ya tsaya a gefen kabarin mutane suna
kallansa.
Sai yace saboda mamaki da rudewa da tsoro da firgita wasu
saida suka suma awajen. Daga karshe dai malami yace ina
'yan uwansa da hukuma su yarda da asashi cikin kabarin
duk suka amince!!!
Koda aka zo da gawar aka sata cikin kabarin, Sai Macijin yayi
wata Girgiza mai karfi ya ya shiga cikin kabarin ta cikin kasa,
nan take wadanda suka sashi suka fito a guje cikin firgita da
rudewa! Koda aka leka cikin kabarin sai akaga Macijin ya
fara Nade mamacin daga kafarsa har zuwa kansa,
yana gama nadewa, ya matse shi kana jin karar irin yadda
Kashin gawar yake kara yana haduwa baras, baras! can da
mukaji shiru sai muka leka mu gani sai muka ga Macijin
yananan a zagaye da Gawa. Ganin irin wannan hali da ake
ciki sai malamin yace Babu yadda zamu yi illa mu zuba kasa
kawai mu rufeshi, sai muka aikata hakan.
Bayan da muka dawo gidansu sai malamin ya tambayi
Mahaifin Yaron (saurayi)
SAI BABAN YACE SHIDAI WANNAN YARON YANA DA BIYAYYA
GA IYAYANSA, SAI DAI BAYA YIN SALLAH!!!!
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN. ALLAH KABAMU IKON
YI MAKA IBADA AKAN LOKACI ALLAH KA AMSA MANA IBA
DUNMU BAKI DAYA. Ameeeeen ya rabbi