Rahotanni a Najeriya sun ce jami'an
hukumar tsaro ta SSS sun kai samamen ne a gidan Kanar Sambo Dasuki dake
Abuja babban birnin kasar, sannan wasu jami'an hukumar kuma suka gudanar
da irin wannan samame a gidan mahaifinsa dake Sokoto.
Kwanaki
hudu kenan da sauke Kanar Sambo Dasuki daga mukamin mai bai wa gwamnatin
Najeriya shawara kan sha'anin tsaro, ya bi sahun mutanen da suka hadu
da fushin hukumar tsaro ta farin kaya a kasar SSS.
Rahotannin sun
ce jami'an hukumar ta SSS sun kai samamen ne da marecen ranar Alhamis,
inda suka bukaci sojojin dake gadin gidan sa a Abuja da su basu wuri su
yi abinda ya kai su.
A cewar rahotannin, jami'an hukumar sun ce
sun je gidan ne domin su samu ganawa da Kanar Sambo Dasuki dangane da
wasu lamura, inda har su ka yi barazanar kutsawa cikin gidan da karfi
idan aka ki basu hadin kai.
Kawo yanzu dai babu wata hukuma ta
gwamnati data fito fili ta ce wani abu dangane da wannan kawanya, amma
wata majiya ta tabbatar wa BBC wannan lamari.
Title :
Dss Sun kama Sambo Dasuki
Description : Rahotanni a Najeriya sun ce jami'an hukumar tsaro ta SSS sun kai samamen ne a gidan Kanar Sambo Dasuki dake Abuja babban birnin kasa...
Rating :
5