Wani dan kunar bakin-wake ya tada bomb a cikin garin Potiskum dake jihar Yobe.
A safiyar yau Lahadi ne mazauna garin Potiskum suka shiga cikin fargaba, sakamakon tada bomb din da wani dan kunar bakin wake yayi.
Inda wani mazaunin garin ya shaidawa 1AREWA cewa; "Bomb ne ya shafe, inda wani dan kunar bakin wake ya tayar a cikin wata Coci a unguwar Jigawa dake Potiskum din".
Amma har yanzu ba'a bayyana adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba, ku kasance tare damu domin jin halin da duniya take ciki..