Labarin tsoho ya sa ni zubar da hawaye saboda dalilai kamar haka:
---------
1. Lokacin da na karanta labarin hadisin manzon Allah na fara tunowa dangane da sada zumunta wa masoyan mahaifi ko da bayan mutuwarsa, wannan ya sosa min rai sosai ganin Kafiri yai aikin da yawancin musulmi yanzu ba su iyawa.
------------------
2. Na tausayawa tsoho kuma sai na tuna da yawan tsaffin da suke nan Nigeria masu karban fansho wadda basa karban daya bisa hudu na abin da wannan tsoho ke karba amma haka suke rayuwa.
------------------------------
3. Duk tattalin arzikin da aka gina shi kan cin riba da kudin ruwa ba shi da albarka kuma komai kyan sa wata rana sai ya rushe, amma turawa sun kasa fahimtar hakan. Don Allah in ka san wani mai karban bashin kudi na ruwa, musamman ma daga banki ka duba rayuwarsa ka gani ya yake gudanar da ita? Mafi yawancinsu na shiga cikin kunci da damuwa da dimuwa sakamakon irin wannan tsinannan bashi marar albarka.
-------------------------------------
Allah ya ganar da mu hanya madaidaiciya ya raba mu da sharrin riba da wakilanta.