Shugaban Najeria, Muhammadu Buhari, ya amince da wasu shirye shiryen ceto jihohin kasar da suka kasa biyan albashin ma'aikatansu.
Shugaba Buhari ya amince a raba $1.7bn daga cikin $2bn da ake da su a cikin asusun rarar man fetur na kasar a yunkurin da ake gani zai sa jihohin kasar su farfado daga cikin mummunan yanayin rashin kudin da suke ciki.
Rahotanni sun ce shugaban ya umarci babban bankin kasar ya bullo da wani shiri na musanman, wanda za a samar da kudade da za su kai N300bn domin bai wa jihohin a matsayin bashi mara tsauri.
Kazalika, shugaban Najeriya ya amince da wani tsari na rage wa jihohi radadin biyan basussukan da suka suka ciwo, wanda zai sa su rika amfani da kudaden a wasu fannoni na bunkasa jama'arsu a maimakon biyan bashi gaba daya.
Kimanin jihohi 12 ne dai daga cikin 36 na kasar aka bayar da rahoton ma'aikatansu na bin su bashin albashi na wata da watanni da kuma wasu kudaden alawus, da jumullarsu ta haura N110bn.
Wata majiya daga gwamnati ta ce kudaden da ma'aikata ke bi bashi a kasar sun kai N250bn, domin akwai wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya da su ma ba a biya su ba wata da watanni.