Rahotanni daga Chadi na cewa mayakan Boko Haram sun hallaka mutane fiye da 20.
Hukumomi sun ce mayakan sun kaddamar da hare-haren ne a kauyuka biyu da ke kusa da tafkin Chadi.
A kauyen, Merom 'yan Boko Haram din sun yi wa maza 13 yankan rago a cikin dare.
Daga nan sai suka je kauye na biyu inda suka hallaka wasu makiyaya.
A cikin makwannin nan 'yan Boko Haram sun tsananta hare-hare a Nigeria.
Ta kai hare-hare a Chadi a cikin wannan watan musamman a Ndjamena babban birnin kasar.