A Najeriya, daruruwan 'yan kasuwar kudu
maso gabashin kasar sun ki bude
kasuwanni a wasu jihohin shiyyar a
matsayin wani mataki na nuna adawa da
kai wasu fursunonin Boko Haram yankin.
'Yan kasuwar sun yi dafifi a bakin kasuwar
garin Ekwulobia na jihar Anambra, inda ake
zargin an kai fursinonin gidan yarin garin.
'Yan kasuwar sun bayar da sanarwar rufe
illahirin kasuwannin yankin na tsawon yini
daya, a matsayin wani gargadi na neman a
hanzarta kawar da fursunonin na Boko
Haram daga gidan yarin.
Kazalika, an rufe kasuwanni a jihar Enugu,
sai dai rahotanni sun nuna cewa kasuwanni
sun kasance a bude a jihohin Abia da
Ebonyi da Imo.
'Yan kasuwar sun ce suna jin tsoro kada
'yan boko Haram su kai musu hari idan aka
ci gaba da tsare mutanen a yankin.
Title :
Boko Haram: An ki bude kasuwanni a Enugu
Description : A Najeriya, daruruwan 'yan kasuwar kudu maso gabashin kasar sun ki bude kasuwanni a wasu jihohin shiyyar a matsayin wani mataki na nu...
Rating :
5