Belgium ta fitar da wasu mutane 250 galibinsu Kiristoci 'yan gudun hijirar Syria daga birnin Aleppo da yaki ya yi wa raga-raga a wani aikin sirri.
Wani kakakin gwamnati ya ce an gudanar da aikin ne a cikin watanni biyu a wani amsa kiraye- kirayen taimakawa Kiristoci da sauran mutanen da suka makale a Aleppo tare da barazanar muzguna masu.
Kungiyoyin masu fafutika ne suka fitar da 'yan gudun hijirar wadanda suka hada da Yazidawa,ta budaddiyar hanya daya tal wacce ke kaiwa kan iyakar Lebanon daga Aleppo.
Daga nan Ofishin Jakadancin Belgium a Beirut ya hadu da su sannan ya kai su Belgium a inda wasunsu ke da dangi, kuma za su iya neman mafaka.