Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufa'i ya ce mutane 20 ne suka mutu sanadiyar harin da aka kai a Sabon Gari Zaria ranar Talata.
Gwamna Elrufai ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa da harin da 'yan ta'addan suka kai.
Gwamna Elrufai ya kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna tana hada gwiwa da gwamnatin tarayya domin kawo karshen ta'addanci a jihar, dama Nigeria baki daya. Ko me zakuce game da wannan al'amari?