Sakataren harkokin tsaron Amurka zai kai ziyara Isra'ila a yau inda daga bisani kuma zai wuce Saudia da kuma Jordan.
An bayyana ziyarar ta sa matsayin wata hanya ta kara samun dai-daito a tsakanin kasashen da suke da hannun a yarjejeniyar da aka cimma kan shirin Iran na makamashin nukiliya.
Ashton Carter zai kuma tattauna da jami'an Isra'ila kafin ya gana da firaminista Benjamin Natanyahu a ranar talata.
Tuni dai Mr Natantahu ya ce yarjejeniyar da aka cimma akan shirin Iran din anyi babban kuskure a tarihi.