========
Mu'awuyatu Ibn Hakam Assulami, wani Sahabi ne daga mutanen Hijaz da ke ziyarar Madina.
-------
Mu'awiya Ibn Hakam ya ce, Wata rana ina sallah tare da ma'aikin Allah sai wani mutum daga cikin mutane ya yi atishawa, ni kuwa nace masa Yarhamukallahu, sai mutane suka harareni, sai nace kaicon mahaifiyata, menene damuwarsu suke hararana?
Sai suka fara bugun tafukan hannayensu a cinyoyinsu, da na ga suna sa ni shiru ne sai na rufe bakina nai shiru.
Da ma'aikin Allah ya yi sallah, fansarsa mahaifiyata, ban taba ganin malami da ya iya koyarwa kamarsa ba, Wallahi bai harareni ba kuma bai dokeni ba bai zage ni ba, ya ce: "Wannan Sallah da kake gani babu wani zance na mutane da ya dace da ita, kawai abin da ake yi cikinta tasbihi ne da kabbara da kuma karatun Al-kur'ani".
--------------------
Muslim da Abu Dauda da kuma Nasa'i suka ruwaito.