Daruruwan mata daga ko'ina a jihar Sokoto sun nuna goyon bayansu da karramawa ga tsohon mai baiwa Shugaban kasa shawara a lamarin tsaro, NSA Sambo Dasuki tare da yi masa fatan alheri ga yanayin da ya shiga.
Hajiya Kulu Abdullahi Rabah, Ko-ordineta ta Mata Yan Siyasa a jihar Sokoto ce ta furta hakan a cikin wata hira da ta yi da ‘yan jarida, inda aka buga a Jaridar Pilot ta Ranar Lahadi.
Ta ce, “Sanin daraja da mutunci na NSA Sambo Dasuki a matsayin jinin Mujaddadi Usumanu Dan Fodio da kuma irin tsare gaskiya da amana ya sanya mata a jihar Sokoto ba za su yi masa butulci ba, kuma za su ci gaba da sanya shi addua don neman tsari da kariya da kowane irin zalunci da za a yi masa a nan gaba”.
Hajiya Rabah ta kara da cewa ba don wata kiyayya ta addini ko rashin aiki tukuru ne wasu ke yi masa tozartawa ba, sai don yaki ya bi Buhari ko nuna goyon bayansa ga APC, wanda kuma hakan ya zama tamkar cin amana ga wanda ya nada shi a bisa mukaminsa.
Hajiya Rabah ta nemi Gwamnatin Buhari da ta san cewa komai nisan jifa zai fado, kuma komai nisan dare gari zai waye.
“Yin adalci, tsare gaskiya da kuma kiyaye wa daga zaluncin komai kankantarsa shine mutunci da amana ga mai mulki. Don haka Buhari da masu goyon bayansa ga cin mutuncin masu yi masa adawa su hankalta' inji Kulu Rabah.