Kungiyar ta ce ta kaddamar da Facegloria ne domin hana batsa da kalaman batanci.
Wata kungiyar masu wa'azin Kirista a Brazil ta kaddamar da wani shafin sada zumunta na zamani wanda ba za a rika yin rantsuwa da yin batsa a cikinsa ba.
Kungiyar, mai sunaFacegloria, ta yi ikirarin cewa tun da aka kaddamar da shi a watan jiya, shafin ya samu mambobi 100,000.
Kungiyar ta haramta yin amfani da kalmomi 600 a shafin, sannan akwai wani madanni mai suna "Amin" wanda mutum zai latsa idan yana so ya yaba kan wani abu da ya burge shi a dandalin.
A shekarar 2013 ma, wata kungiyar Musulmai mai suna Ummaland ta kaddamar da irin wannan dandali, inda a yanzu take da mambobi kusan 329,000.
Wasu daga cikin abubuwan da ta ware su ne "Wani gurbi da ba zai ba da dama a rika ganin abubuwan da mata ke wallafawa, da kuma kuma wallafa jawabai na fadakar da mutane.
Wasu daga cikin mutanen da suka kaddamar da shafukan, Maruf Yusupov da Jamoliddin Daliyev sun ce "Mun samar dandalin sada zumunta na Ummaland bisa tsarin addinin musulinci: babu gulma, ko cin naman mutane; muna mayar da hankali ne kan abubuwan da suka dace".
Yada addini
Shi dai dandalin sada zumunta na Facegloria ana yin amfani da harshen Portuguese ne wajen sadarwa, amma ana sa ran za a fara amfani da wasu harsunan nan gaba kadan.
Kasar Brazil ce ke da mafi yawan mabiya darikar Roman Katolika.
Atilla Barros ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa "Za ka ga hotunan tayar da hankali da na batsa a Facebook.Hakan ne ya sa muka kudiri aniyar samar da dandalin sada zumuta a shafin intanet domin isar da sakonni game da addini da abubuwan da Allah ya ke cewa."
Kazalika, an haramta watsa hotunan masu auren jinsi guda a dandalin.