Rundunar 'yan sandan Daular Larabawa ta ce ta kama 'yan Najeriya uku masu kutse a shafin intanet a bankunan Amurka.
An kama mutane ne bayan 'yan sandan sun samu labarin masu aikata laifin kutsen daga rundunar 'yan sanda ta birnin California da ke Amurka.
Ana zargin masu laifin ne da kutse a cikin sakonni da wuraren ajiyar kudi a shafukan intanet, inda suke sato takardun sirrin mutane da na ma'aikatu a Amurka.
'Yan sanda sun kai wa masu kutsen hari a wata maboyarsu da ke masarautar Ajman, inda suka gano jerin lambobin ajiyar kudi a bankin intanet na mutane sama da miliyan biyar.
Shugaban 'yan kutsen na da shekaru 24, mabiyan sa su biyu kuma duk shekarun su 26, kuma dukkansu sun shigo kasar Larabawan ne yawon bude ido.