Yan sanda a Kano a Nigeria sun tabbatar da cewa wata yarinya da ta kai harin kunar bakin wake a daidai shataletalen 'Dangi' ta rasa ranta, sai kuma mutum guda da ya jikkata.
Harin ya auku ne wasu 'yan mintina bayan kammala sallah Taraweeh a wani masallaci dake kusa da shataletalen.
Wani ganau a Kano ya ce ya ga motocin daukar marasa lafiya da kuma 'yan sanda a inda aka kai harin
Wani ganau ya shaidawa wakilinnamu cewa yaga wata yarinya a lokacin da take barin masallacin bayan kammala sallar, sannan bayan fashewar bam din, ya ga sassan jikinta a kasa.
Ya ce wani mutum ya jikkata a lokacin da yake kokarin tserewa