Bayan da aka buga wasannin mako na 16 a gasar Premier Nigeria, an ci kwallaye 36 a bugun fenariti 41 da alkalan gasar suka bayar.
Kungiyar Enyimba ce ta fi samun yawan fenariti a gasar, inda ta samu guda hudu ta kuma zura su a raga.
Jumulla an ci kwallaye 326 daga wasanni 157 da aka buga, bayan da aka kammala wasannin mako na 16 a gasar.
Sunshine Stars wacce ke mataki na daya a teburi da maki 30, ta fi yawan zura kwallaye a gasar, a inda ta zura 25 a raga.
Kungiyar Taraba FC wacce ke matsayi na 20 a teburin Premier, ta ci kwallaye 14 kacal, yayin da aka ci ta kwallaye 21 a gasar.