Humaidu Ibn Abdurrahman Ibn Auf ya ce, ya ji Mu'awiyata Allah ya kara masa yarda shekarar da yaje hajji a kan minbari ya karbi wani curin gashi wacce take hannun wani dogari sai ya ce; Mutanen Madina ina malamanku? Na ji manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam yana hani a kan kwatankwacin wannan, kuma yana ce wa: "Banu Isra'ila dai sun halaka ne lokacin da matansu suka riki wannan".
Bukhari da Muslim suka ruwaito.
----------------------------------------
Mata kuji tsoron Allah ku daina karin gashi a kan ku, kun dai ji daga baki mafi tsarki a duniya, bakin da ba ya karya, yin hakan na jawo halakar al'umma. Mu sani kuma wajibi a kan duk wadda ya ga ana wani abin da bai dace ba yana da ikon yin magana don a gyara yayi hakan.
-----------------------------------------
Allah ya taimakemu ya rabamu da sharrin Iblis.