1. GIRMAN KAI : Shi ya janyo ma Iblees Tsinuwar Allah ta har abada. Alhali da chan shi bawan Allah ne Salihi. Amma da yayi girman kai, Allah bai kyaleshi ba.
2. KWADAYI : Shi ya sanya Babanmu Annabi Aadam (as) yaci bishiyar nan wacce Ubangiji yace kar yaci. Sakamakon haka aka fiddashi daga Aljannah wacce take sama ta bakwai zuwa doron Qasar cikin wahala, shi da zuriyarsa.
3. HASSADA : Shi ya sanya 'daya daga cikin 'ya'yan Annabi Aadam ya kashe 'Dan uwansa. Sakamakon haka ya zamanto shine farkon wanda ya sa'ba ma Allah daga cikin Zuriyar Annabi Aadam (as).
Kuma tun daga lokacin har zuwa Qarshen duniya duk wani kisan kai da za'ayi sai an bashi Kamasho..
********************************
'Yan uwa dukkan wadannan Qissosin Allah ya kawo mana su acikin Alqur'ani ne domin mu karanta, muyi tunani akansu, su zama darasi agaremu acikin wannan rayuwar.
ABINDA NA LURA DASHI :
- GIRMAN KAI : Yana janyo fushin Ubangiji. Kuma duk mai yinsa yana jayayya ne da Allah. Don haka Allah ba ya rangwanta masa.
- KWADAYI : Yakan janyo ma mutum jin kunya agaban Ubangijinsa. Amma Ubangiji yana saurin gafartawa.
- HASSADA : Tana makantar da zuciyar mutum har ya kasa gane gaskiya koda ya santa. Kuma mutum yakan samu Qaskanci na har abada, da kuma zubewar Mutuncinsa.