Addu'ar nan wacce akeyi yayin fara Jima'i tana da mutukar Muhimmanci sosai wajen samun kariya gareku ku ma'aurata, da kuma zuriyarku wacce zaku haifa.
Yazo acikin Sahihul Bukhariy acikin KITABUL WUDHU'I, akan lambar hadisi na 141. Da kuma Sahihu Muslim akan lambar hadisi na 116, da kuma na 1434. Abu Dawud ma ya ruwaito wannan hadisin akan lamba ta 2,161. Ibnu Maajah ma ya kawoshi acikin KITABUN NIKAHI. Imamu Ahmad shima ya ruwaito hadisin acikin MUSNADU juzu'i na farko, shafi na 220, 217, da kuma na 283.
Duk sun ruwaito daga hanyoyi ingantattu daga Manzon Rahama (saww) yana cewa:
"IDAN DAYANKU YAJE MA IYALINSA YACE 'BISMILLAHI, ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAITANA WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAQTANA"
Idan aka Qaddara musu rabon yaro (acikin wannan Jima'in) to shaitan ba zai iya chutar dashi ba. HAR ABADA".
Ga fassarar addu'ar tare da Qarin bayani :
"DA ALBARKAR SUNAN ALLAH (ZAMU FARA WANNAN JIMA'IN) YA ALLAH KA NISANTAR MANA DA SHAITAN (KAR YAZO KUSA DAMU) KUMA KA NISANTAR DA SHAITAN DAGA WANNAN ABINDA ZAKA AZURTAMU DASHI".
Kunji daga bakin da baya Qarya, cewa duk wanda yayi wannan addu'ar kafin fara jima'i, Allah zai tsare yaro ko yarinyar da aka samu ta wannan jima'in daga sharrin shaitan. Shaitan ba zai iya chutar da yaro ko yarinyar ba, har abada.
Na san wasu zasu tambayeni To idan mutum ya kasance ba ya yin wannan Addu'ar Mai zai faru?? To ga amsarku nan: Daga Mujahid (Almajirin ABDULLAHI BN ABBAS R. A) yana cewa:
"IDAN MUTUM YAYI JIMA'I BA TARE DA YA AMBACI SUNAN ALLAH BA, ALJANU SUNA NADEWA AZZAKARINSU AJIKIN NASA. SAI SUYI JIMA'IN TARE DASHI....".
– Aduba cikin NAWADIRUL USOOL na Hakimut Tirmiziy, shafi na 116, da na 243. Da kuma DURRUL MANTHOOR na Imam Jalaluddeen Suyutiy juzu'i na shida, shafi na 148. Da kuma Tafisirin Ibnu Jareer, shafi na 28, da kuma na 88.
Hakika duk yaron da ya zamto kunyi jima'i tare da shaitanun Aljanu har aka samu cikinsa, tabbas ba zai ji maganar mahaifansa ba, ba zai ji tausayinsu ba, Kuma ba zai ji kunyar Allah da Manzonsa acikin rayuwarsa ba.
Don haka yin addu'a kafin saduwa hanya ce babba ta samun ingantacciyar Zuriyyah wacce ba za'a sha wahala wajen tarbiyyarsu ba.
Kuma babbar hanya ce ta kiyaye yaranka daga shafar Aljanu da sauran hanyoyin da shaitanu suke chutar da 'Yan Adam