soyayya tai soyayya tsakanin Jameela da Mussadik har takai mutane na kwatancensu.Ranar da Jameela zata koma makaranta,dukkansu saida sukayi zazzabi,haka suka rabu tana kuka shima yanayi. Ranar da Jameela ta koma makaranta,kowa ya dawo dama ta kara sati daya a gida.Suna tsaye dai dai kofar comm market,sai ga wasu gayu su biyu,Abubakar da samaila.Suna karasowa ziya tace"oh big boys kune haka?samaila ya juya p cap dinsa baya yace"kinganmu dai Queen,amma wannan mai zafin da kuke tare da itafa?Ziya tayi murmushi tace"kawatace ,yace sunantafa?tambayata dakanka.Ya matsa kusa yace"Hajiya sannufa!tawurga mai wata harara tace"ina ciwone zakacemin sannu ko aiki kaga inayi?Yayi murmushi yace"Haba hajiya ai basai mai ciwo ake yiwa sannuba,to amma kiyi hakuri,dan Allah idan bazaki damuba zan iya sanin sunanki?Ta dan ja da baya sannan tace"mezakayi dashi?yace hm inaso ya zama sahun farkone acikin abubuwan da zuciyata zata rika bege a kullum.Hm to an rigaka,domin a yanzu akwai zuciyar da tawa ta narke acikinta,koni bani da iko da sunana ko zuciyata,waccan zuciyar itake da iko da duk rayuwata da ni kaina.Hm amma meye sunan wannan lucky guy din da kika bawa matsayi haka.Ta dubeshi tace"Sunansa Mussadik,shine jina da ganina,shine tunanina,shine ruhina,domin ko yanzu gangar jikina kawai kuke gani,amma zuciyata da ruhina duk suna tare dashi.Samaila yayi murmushi,yace"Oh!abin mamaki baki fadimin sunankiba amma kin fadamin nashi.Hm ai dan karka zake dayawane,kasani ba wani sauran gurbi azuciyata sonsa ya mamaye ko ina.Hm to amma ai ma iya zama abokai idan bakiyarda munzama masoyaba?Hm a'a ai ni Mussadik shine komai nawa.Hm ziya wannan kawartaki kisa baki ta zama kawata mana. Ziya tace"Haba Princessess Meela ki daure kuzama abokai mana.Jameela tayi dariya tace"tunda kin fadmin sunan da masoyina yake fadamin ai yaji sunana ko?to kin yarda muyi abota?tace um um e to,ziya tace rabu da ita tayarda,duk suka sheke da dariya. Kawancen ziya da Jameela yayi karfi sosai domin yanzu komai tare sukeyi,ko ummi da take yar uwarta basa yawo tare sai da ziya. Ziya Bello,yarin yace kyakyawa fara gata doguwa,suffofinta basu zanu da alkalami ba domin in kaganta kamar ita tayi kanta,gata dason mutane,ga fara'a,ko ina tawuce kaji ana zeegal.Amma wayanda suke cikin kungiyarsu suna kiranta da Queen B. Wata rana ziya tasa heater,sai suka fara abinda suka saba ita da wata kawarta hankalinsu ya gushe,ta manta da heater kawai sai wuta ta kama,da kyar suka futa daga dakin,komai na dakin ya kone.Kowa tausaya mata yake yanai mata jaje,amma ita ko ajikinta.Jameela tace da ita ta dawo dakinsu,tace to,suka sanar da Ummi itama ta tausaya muta. Bayan ziya ta dawo dakinsune,kashe gari sai gawata katuwar mota ta faka gaban Queen Amina hostel,direban na tsayawa ya futo da gudu ya bude motas,wata kyakyawar macece,ta futo,tana futowa ta kira waya,kamar minti hudu sai ga Ziya da Jameela sunfuto,suna zuwa gurinta,ita da ziya suka rungume juna kamar tuf da taya,kai kace namijine da mace sha'awarsu ta motsa. Ziya tace"safeena wannan itace kawata Jameela da nake baki labari,Jameela wannan itace Safeena danake baki labari. Jamella tace"waw kece safeena?gaskiya ko yaushe sai munyi zancenki,tayi murmushi tace"hm kece Jameela gaskiya kin hadu,suka bude bayan motar suka debo kayan sawa dana abinci dayawa suka shiga hostel. Suna shiga dakin Safeena tace"oh ammafa da zafi,baku da A.c ne a dakin,ziya tace babu dakinnasu ai sai a hankali. Safeena tace"to ai tunda kin dawo dakinsu yakamata asa,da nasan babu ma dana tawo muku da ita,Jameela tai murmushi tace angode,ta dubeta tace meye na godiya ai mun zama daya tunda kina tare da Queen B. Safeena tace"ta ya dakinnaki za'a gyarashine koko zaki kama wani a wajen makaranta?ziya tayi murmushi tace"umm zan duba nan da sati biyu in gani,amma gaskiya ma dai wajen makaranta zanje in kama daki kawai zaifi.Jameela tace haba ga daki ki zauna ko ba hakaba.Ziya tace haba daki mutum uku ai munyi yawa duk dacewa yanada girma,amma ai muna bukatar sakewa ko. Bayan sunci abinci sun hutane,Suka rako Safeena,zata tafi ta dakko waya Black berry tabawa Jameela da kudi dubu talatin,tace ta kashe,Jameela tai ta godiya kamar ta hadiyeta. Suna komawa daki sukai ta bude kayan da Safeena ta kawowa ziya,dinki masu tsada akwati biyu cike,ga ta kalma kala kala,ga waya irinta Jameela,abin mama jiya ziya tayi gobara amma yau tasami fiye da abin data rasa gashi nima har na samu nawa,Jameela ke fadin haka a zuciyarta,tana rufe baki,ziya ta dakko dinki kala goma tace kidauki wannan kema kyarika sawa, mur kamar anbiya mata saudiyya,dama tanason irin kayan da ziya kesawa sai dai tasan da tsada ko dinkin ma balle kayan to yau dama tazo. Bayan sati biyu,wata rana,Ummi ta je gida week end,Jameela ta dawo lacture ta gaji tana cire kaya ta dan tafasa indomie taci,sai ta kwanta,Ziya na dawowa,taga Jameela kwance daga ita sai Bra da pant,sai ko tai wata ajiyar zuciya,ta zaro ido kamar zakin daya shekara baici namaba ya hangi barewa.