TAMBAYA TA 1617
*******************
slm malam don allah ka taimaka min ni bana sha'awar mace sai namiji kuma wlh ban taba neman namiji ta dubura ba. kuma na kan fi shekara ban kusanci wani ba. duk da akwai masu son yin hulda dani amma nake guje musu. matsalata daya itace yadda zan daina jin feeling a rai na..
Tun watan uku na turo maka da wannan wasikar amma har yanzu baka amsa min ba.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Yana daga cikin makircin shaitan da kutungwilarsa, ya Qawatar maka da ayyukan sa'bon Allah acikin zuciyarka, koda ka san cewa Allah ya hana, amma ba zaka iya bari ba. saboda rudin shaitan.
Shawarar da zan baka anan ita ce:
- Kaji tsoron Allah wanda ya halicceka alhali da chan babu kai. Kuma ka tuna cewa akwai ranar da zaka koma gareshi domin karbar sakamakon ayyukan da ka aikata.
- Ka sani cewa LUWADI wani irin Qazamin zunubi ne wanda koda dabbobi suna kyamarsa. Kuma Allah ya kifar da al'ummah guda saboda bala'in wannan zunubin da suka aikata.
- Manzon Allah (saww) ya Qirga 'yan Luwadi acikin mutanen da ko yaushe suna cikin fushin Allah. Allah ya riga ya tsine musu kuma ba zai kallesu da rahamarsa ba.
- Kayi kokari ka yawaita istigfari, Hailala, karatun Alqur'ani, da sauran ayyuka na kwarai domin samun dacewa da karbar tubanka awajen Allah.
- Ka chanza abokanka, ds wuraren zamanka, kuma ka nisanci duk masu irin wannan halayen. ka abokanci mutanen kirki.
- Kaje kayi aure, idan baka da dama ka yawaita azumi. Kuma ka rika tuna kusan in Ubangijinka gareka.
Allah ya shiryeka. Mu kuma Allah ya Qara nesantar damu daga kowanne ALKABA'IR.
WALLAHU A'ALAM.