wani saurayi ne suna soyayya da budurwarsa maisuna ummi sun shaqu sosaai rannan iyayenta
suka tuntubeshi da maganar aure
Abin takaici shine saurayin nan baida ko bulo saboda baida sana,a
yayi diploma ba aiki ummi kuwa tace batason kowa saishi
Iyayen ummi sukace sunbashi wata biyu yasamu sana,a kosu aurar da yarsu saboda tsananin so da ummi kemasa yasa kullum
idan aka
bata naira dari biyar nazuwa skul da breakfast saita tafi a kafa tayini da yunwa tariqa tara masa kudin
har tsawon wata guda kana ta bashi
tace ga wannan kanemi sana,a koyaya ne musamu muyi aure
bayan yakarbi kudi yafara siyarda takalmi da jaka akan titi har yayi shagonsa nakansa rannan saiwata
katuwar mota ta faka kofar shagonsa wata budurwa tafito ta siya takalmi da jaka
saita duba ta manto jakar
kudin ta gida taroqe shi yabita gida ya karbo kudin suntafi a mota tace masa sunana maryam
tatambayeshi
labarinsa kaf yagaya mata saita tausaya masa saurayi kamarka yayi karatu babu aiki bayan ya karbo kudinsa yadawo gida yayi wanka
yashirya zai tafi gidansu ummi maganar aurensu
Saiga dan aike da emblop yakarba yafara karantawa daga maryam
nayi magana da babana kuma nafada masa kai nakeso nasan zakai mamaki babana yayi alqawari zaibaka MD manajan darakta na kamfaninsa inhar zaka aureni yabaka kwana biyu
WAI IDAN KAINE WAZAKA AURA ummi KO maryam ??