A wani lokaci a yau din nan Asabar ce ake sa ran shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Afirka ta Kudu don halartar taron shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka karo na 25 da ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudun.
A wata sanarwa da babban mai ba wa shugaban na Nijeriya shawara kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya ce shugaba Buharin zai jagoranci taron kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirkan da za a gudanar a yau din Asabar, kamar yadda kuma zai gana da shugabanni da manyan jami’an kasashen Afirkan a kokarin da ya ke yi na fada da kungiyar nan ta Boko Haram da kuma tabbatar da tsaron kasashen yankin.
A wata sabuwa kuma a daren jiya Juma’a shugaba Buharin da uwargidansa Hajiya Aisha Buhari sun gana da wasu daga cikin iyayen ‘yan matan nan na Chibok da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace samar da shekara guda da ta gabata.
Matar mataimakin shugaban Nijeriyan Dolapo Osinbajo ce ta shaida wa manema labarai labarin ganawar inda ta ce shugaban da uwargidansa sun bayyanawa iyayen damuwarsu dangane da halin da ‘ya’yan na su suke ciki da kuma tabbatar musu da kokarin da gwamnati take yi wajen ganin an kwato ‘yan matan daga hannun ‘yan Boko Haram din.