Hakika duniyar nan bata taba ganin mutum cikakke kamar Manzon Allah (saww) ba.
Shi kadai shine:
* Shine Shugaban Al'ummarsa.
* Shine Alkalinsu.
* Shine Likitansu.
* Shine kwamandan Yakinsu.
* Shine masanin kimiyyarsu.
* Shine Malaminsu mai koyar dasu harkar addininsu da duniyarsu, kuma shine jagoransu cikin dukkan sha'aninsu. Amma fa duk da haka bai koyi komai awajen kowa ba.. Amma kowa awajensa yake koyon komai. (saww).
ANNABI ne UMMIYYI (MAI TAQAMA DA WAHAYI) BA YA RUBUTU KO KARATU AKAN TAKARDA. SHI RUBUTUNSA AZUKATAN AL'UMMARSA YAKE YI.
Ya Allah ka Qara mana son MANZON ALLAH (SAWW).