Ina futowa wanka nasa towell ina share jikina sai najiyo kira kamar daga sama,tun ina jinkiran daga nesa har yazo kusa nayunkuro zanfuto na amsa momina takomar dani dakina tasa kwado ta kulle,ina lekowa ta wundo sai naga mahaifina cikin kakinsa na conel shi da shamsiyya da mahaifiyarta.Suna shigowa falo ya dubi mahaifiyata cikin tsananin fishi yace"ina Mubarak yake?tace dashi meke faruwa?ya dubeta yace bansaniba kedai kawai kisanar dani ina yake?mahaifiyata tace"yaje filin kwallo to amma meya faru?mahaifina yayi wani juyi irinnasu na sojoji yace"ai waka abakin mai ita tafi dadi gatanan tambayeta meyafaru.Mum dina takama hannun shamsiyya tace yata sanar dani meke faruwa?shamsiyya takasa magana har saida mahaifiyarta ta kai mata magangari tace bazakiyi maganaba?sannan shamsiyya ta fashe da kuka tace"cikine dani"mum dina tayi wani dogon salati tace?waye yayimiki"shamsiyya tayi wuki wuki da ido,momina ta kara tambayarta wai waye yayi miki?tayi shiru.Mamanta ta maketa tace bazaki fadaba?ta fashe da kukan muna funci tace"mubarakne".
Ina tsaye cikin dakina ina jin tace ninaimata ciki naji kamar nai fitsari a wando tsabar furgita,nan danan nayi gumi kamar an watsamin ruwa.
Momina tace da ita ke shamsiyya kiji tsoron Ubangiji,karkiyiwa dana sharri,mahaifina yayi wani ihu irin nasojoji yace"yi mana shiru,watau duk gargadin da nakewa wannan yaron na kar yakula mata ya sa karatunsa gaba a banza,to yau zai dan dana kudansa,kuma wannan yarinya sai ya aureta tunda diyar abokinace kuma ko yanaso ko bayaso sai ya aureta.
Narasa ta ina zanbi ingudu nasani lallai idan yakamani to wallahi ko na lahira sai ya fini jin dadi,na leka wundona naga nisan tsawon saman benen da nake zuwa kasa,wayyo sai naji inama ace na mutu a lokacin dana huta,dominko bani da zabi,dole na aureta,kuma nasan sai ya kusa sati biyu yana bani wahala irin tasu ta sojoji.
Narasa mafita,nasake lekawa naga tsawon benen saiko na dauki jakar goyawata na cusa kaya bansan ko kala nawama na daukaba,naja dabaya nayo tsalle daga kan benen ta wundon dakina na fado bayan gidanmu,cikin hanzari nayi ta maza namike nakama gudu,nanda nan na nufi tashar mota batare da nasan garin da zan guduba.
Gashi bakudi a hannuna,ina zuwa bakintasha wani dan uniyal yace" samari Ibadan zaka"na dubeshi nai shiru,can sai nace"E amma wallahi bani da kosisi,yace amma nake magana kayi shiru.Nace kayi hakuri inata tunanin zucine,yace to sai dai idan zaka hau trela,nace e zan hau,ya futo dani daga tasha ya dorani kan wata trela,munkai kamar mu goma sha biyu ga lodin kaya.
Ana sallar magriba dreba yayiwa mota key muka dauki hanya,burina kawai nayi nisa kar mahaifina ya turo kuratansa sukamani,zuciyata nata bugawa.
Lokacin da dan uniyal dinnan yatambayeni Ibadan zaka sai nashiga tunani idan naje ibadan gurinwa zanje?sai natuno akwai abokina yana can yana neman kudi.
Dady na yacire kudi dubu ashirin yabawa maman shamsiyya yace sukula da ita nanda kwana uku zai zo ayi maganar biki,tana haihuwa sai a daura aure.Nan suka kama hanya suka fuce daga gidanmu,mahaifiyata tarasa ta ina zata bullowa wannan al amarine.
Tasan mahaifina baya magana ya saba,kuma tasan matsalar data faru tsakanina da shamsiyya to amma ya zatayi ta ganar da mahaifina.Nasan Dady na zaiyi la akkari dacewa shamsiyya budurwatace,sannan babu wanda bai sammu tareba,kuma babu wanda za'ace nai mata ciki bai yardaba in banda yayanta da kawayenta nakusa.
Munyi nisa a hanya,babu abin da nake tunawa sai mahaifiyata domin idan ta fuskanci cewa guduwa nayi zata gasgata cewa nine naiwa shamsiyya ciki.Zuciyata nata kai kawo,ina tunanin irin halin da ni da mahaifiyata zamu shiga sakamakon rashin juna,domin shakuwarmu tawuce in iya musaltawa.
Muna zuwa kwara,naji wasu suna cewa damu"boko haram!boko haram!!sai naji sukuma yan uwana hausawa suna mayarwa da yarbawan martani suna cewa"Ala soka!Ala soka.
Bansan dawan garinba wai amarya tayi kashi a moda,nasaki baki kawai sauraren abin da ake kawai nake.Bayan munwuce zuciyata taki hakura burina naji meye ma'anar abin da s uke fada.Sai na matsa kusa da wani saurayi kamata na tambayeshi meye ma'anar abinda suke fadi sai ko yace dani"yarbawa sunacewa wai hausawa sune yan boko haram,shiyasa idan sungammu sai surika cewa "boko aram"sundade sunai mana wannan cinmutuncin,sai daga baya muma muka gano muke cewa dasu"Ala soka"(yan mafiya)hakan yasa sun rage kiranmu da boko aram.Nayi ajiyar zuciya nace nagode.
Muna isa ibadan cikin dare gashi wayata ba caji,gashi ba inda nasani.kowa ya sauka aka watse sai ni kadai,naje wani guri na tsaya,sai namatsa wajen wasu mata,ina zuwa naga wata yar budurwa,natambayeta da turanci,dan Allah ina ake cajin waya?kafin tabani amsa uwarta tazo ta maketa,cikin yaren yarbanci tace"shegiya bahaushen kikewa magana.Bansan me taceba amma na fuskanci cewa hanata magana dani takeyi,raina yabaci,sai nayi gaba,nakara samun wasu,nakuma tambayar wata itama dakyar uwarta na hanata amma sai da ta fadamin.
HAMZA UMAR IBRAHIM{DIAMOND BOY}