alhji abba ya mike a daga kan kujerar yace
Alhamdillah rana dubu ta barawo rana daya ta me
kaya kagama guje gujen naka amma gashi
nakama cikin sauki' khadijat wadda tuni ta rude
tace kb meke faruwane? Nakasa bata amsa'
tajuya tace Abba kasanshine? Shima baibata
amsa ba' najuya da nufin guduwa amma ina tuni
bodygurd dinsa sukayi caraf dani' ita kuwa
khadijat ta rude sai kuka take tana tambayar
abbanta lpy? Amma yayo waje ko kallanta baiyi
ba' suka sani a mota sai division'
Tuni labari ya watsu ko ina cewa an kama wanda
sukayiwa alhji abba sadik fashi tuni daixad ya
ranta ata kare domin har wajen shayin akaje
amma bayanan' batun kanwata kuwa tazo domin
taganni sau dayawa amma ina sam ba'a barinta
taganni' haka nakasance cikin wannnan hali ina
tunanin mai zai faru dani' ranar litinin itace ranar
daza akaini court domin kuwa sun gama tattara
bayanai' ranar juma'a da yamma ina zaune a sell
ina tunanin halin da kanwata take cikine wani dan
sanda yashigo ya fito dani yace wata tanason
magana dani' kanwata nagani maryam' yallabai
yace minti goma aka baku'
Nakarasa nace nace kanwata kinga yadda Allah
yayi damu ko? Ta fashe da kuka tace yaya yanzu
idan court ta yanke maka hukunci mai tsauri
yazanyi da rayuwata' yaya kaine abbana kaine
ummana bani da kowa saikai' nima bansan sanda
hawaye yafara zuba daga idanuna ba' nakasa
magana kawai kuka nake' khadeejat ce ta karaso
tace kudaina kuka kb nasan bazaka aikata haka
ba kuma insha Allahu daddyna zai fuskance ni
bazai bari a hukunta ka ba' maryam tace dan
Allah aunty na ki taimakeni kisa daddynki yasaki
yaya wallahi yayana bazai aikata fashi ba'
khadeejat ta jata jikinta tana lallashinta' officer
ne yakatsemu yace time ya cika' aka maidani
maryam sai rusa kuka take'
Adaren ranar Asabar ne aka kama wadansu yan
fashi a wata unguwa da akai bincike sai aka gane
cewa sune yan fashin da sukayi fashi a gidan
Alhaji abba sadik' hakan yasa hukuma tayi free
dina' wannan ranar lahadin tazamar min babbar
rana' Alhaji abba sadik da kanshi yadaukeni
amotarsa har gidansa' ina zuwa natarar dasu
daixad khadijat da fateema ina fitowa sukazo
suka tareni' maryam tasaka kukan farin ciki'
muka shiga ciki alhaji yakiramu dakinsa' yafara
magana kamar haka:-
Yace kabir mun zalince ku arashin sani amma
dan Allah ina naiman yafiyar ku' nace Alhji
bakomai wannan abun rubutaccen al'amarine
daga Allah' alhaji yace gaskiya naji dadin wannan
kalamai naka' yanzu ku fadi duk abinda kukeso
matukar baifi karpina ba zanyi muku' na kalli
daixad ya kalleni' daizad yace alhaji taimako daya
zakai mana shine ka karbar wa su kabir
dukiyarsu daga hannun aminin mahaipinsu' alh
yace wannan mai saukine indai kuna da sheda
yanzuma bari nakira lauyana' nace alhaji muna
da duk wata shaida da kotu take bukata' take
yakira lauyansa aka gama shirya komai sai kotu'
Munyi nasara a kotu domin kuwa an kwace
dukkan wata dukiya da kadara an damqa mana
nida kanwata tuni duniya tadawo mana sabuwa
saidai kash! Babu iyaye' tuni na shiga neman
auren Khadeejat ba a dau lokaci ba aka sha
gagarumin biki' maryam tadawo yar gata gurin
khadijat banda karatu ba abinda take' daizad
kuwa yatsaya ruwan ido' nikuwa kullum sai gorin
aure nake masa'
Ina zaune tunanin yarinyar nan da ta taimaka min
lokacin da sojojinnan suka biyoni ya fado min
aikuwa banyi wata-wata ba nakira daixad mu
shiga mota sai gidan mukai sallama yarinyar
nance dai ta fito' tana ganina taganeni tace lah!
Ashe zan sake ganinka? Nace wallahi gani dai'
nace wai ke ina yan gidan naku sukene? Tace
hmm ai ni karatu ne yakawo ni garinnan ba
wanda nasani yanzu hakama nagama' next
month zantapi garinmu' daixad yace inane garin
naku? Tace katsina' daixad yace aikuwa tare
zamu tapi' nace Allah malam? Yace ai nagaji da
gorinnan' itadai dariya tayi kawai' nace wai
yasunanki? Tace ni sunana husna'
Haka kuwa akayi dan kankanin lokaci soyayya ta
Kullu tsakanin daixad da husna lokacin tafiyar ta
yayi yabita katsina bayan ya dawo manya suka
shiga maganar aka daura aurensu daizad' husna
tasamu aiki a asibiti' hak a rayuwar ta ci gava da
kasan cewa cinkin kwanciyar hankali kamar ba
musha wahala ba' dama Allah (s,w,t) yace
dukkan tsanani yana tare da yayewa..........THE
END