Kungiyar Manchester United ce ta fi kowacce kungiyar kwallon kafa daraja a duniya, a wani rahoto da masu bayar da shawara na Brand Finance suka fitar.
Duk da kasa lashe kofi da United ta yi a kakar wasannin bana, an kiyasta cewar darajar kungiyar ta kai sama da dala biliyan 1.
Kungiyoyi shida daga cikin goman farko dake jerin wadan da suka fi daraja a duniya suna buga gasar Premier ne.
Barcelona wacce ta dauki kofin zakarun Turai ranar Asabar tana mataki na shida inda darajarta ta kai dala miliyan 773.
Rahoton ya kuma ce United din za ta iya samun karin kudaden shiga a inda darajarta za ta kara yin sama a shekaru masu zuwa.
United ta samu wannan matakin ne sakamakon kulla yarjejeniyar nuna wasannin Premier a talabijin da ta kai sama da fan biliyan 5.
Bayern Munich wacce a baya ke mataki na daya ta koma ta biyu, Real Madrid tana matsayi na uku, PSG ce ta tara yayin da babu wata kungiya daga Italiya a sawun goman farko.
Title :
Manchester United ce ta fi daraja a duniya
Description : Kungiyar Manchester United ce ta fi kowacce kungiyar kwallon kafa daraja a duniya, a wani rahoto da masu bayar da shawara na Brand Finance s...
Rating :
5