Shi Mutum ne tataccen Launin fatar jiki. Fatar jikinsa tana Qamshi tana haske tana kyalli kamar tatacciyar azurfa.
Gashin kansa baki ne wuluk, Ya shekara sittin da uku aduniya amma gaba daya furfurar dake Jikinsa guda goma sha bakwai ce.
Gashin kansa yayi lufluf, yana sheki, yana Qamshi. Ya sauko har kan kafadunsa. Yakan taje gashinsa, awasu lokutan yakan saisayeshi (wato askewa sama-sama).
Yana da matsakaicin tsawo. Shi ba dogo bane, kuma ba gajere bane. Amma idan ya shiga cikin jama'a shi kadai kawai ake hangowa saboda hasken jikinsa da kwarjinin fuskarsa (saww).
Mafi kyawun salatin Allah ya tabbata ga mafi kyawun dukkanin bayan Allah, shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalansa da sahabbansa