BABBAN MATSIYACIN DA BABU IRINSA Shine mutumin da aranar Alkiyamah zai zo da ladan ayyukansa masu yawa, Har ya fara murnar zai shiga aljannah...
Chan kuma idan aka bincika cikin ayyukansa za'a tarar Ya zagi wancan, ya doki wancan, ya chuchi wasu Jama'ar, ya danne hakkokin wasu, yayi gulmar wadansu, Don haka zasu zo neman hakkinsu akansa, agaban Zatin Ubangiji.
Nan take Ubangiji zai sanya Mala'iku su rika kwasowa ladan wannan mutumin ana biyan wadanda ya zalunta.. Har sai ladan nasa ya Qare amma ba'a gama biyan jama'a hakkokinsu ba.
Don haka sai Ubangiji yasa arika kwaso Zunuban wadancan ana Qara lafta ma wannan mutumin. Da haka, da haka, har sai an kammala biyan hakkokinsu..
ZAUREN FIQHU : Wannan hannunka-mai-sanda ne zuwa ga Jami'an Gwamnati da sauran Shugabanni masu Kokarin danne hakkin al'ummah, da cin amana, da Qarya.
Hakanan Samari masu zama agefen Titi. wannan ya wuce kunyi gulmarsa, wannan ya wuce kun zageshi, etc.
Hakanan mata masu haduwa agidan biki, azauna ana hirar mutane ana cin namansu...
GABA DAYA MUJI TSORON ALLAH mu dena.. tun kafin zuwan wannan ranar da nadama ko tuba ba zasu amfanar da mai yinsu ba!!!