Tun da duniya take, ba'a taba samun tataccen Sadauki irin Manzon Allah (saww) ba.
Domin kuwa shine kadai Sadaukin da ya kama Shaitan da hannunsa guda 'daya rak!!
Ya chafkeshi ya Shakeshi. Har sai da harshensa ya zazzago, yayi niyyar ya daureshi ajikin tike, to amma sai yaji kunyar 'Dan uwansa Annabi Sulaimanu (as).
Sadaukin da ko ranar lahira Wuta take tsoronsa!! Idan tazo tayi Gunji afilin alkiyama, kowa zai zube akan Gwiwarsa. Amma banda SHI (saww).
Wutar zatayi Qas da kanta tace "INA NI, INA KAI, YA MUHAMMADU!!".
Alokacin yakin Khandaq, ana cikin tonon rami sai su Salmanul Farisy suka tarar da wani Dutse mai tauri wanda suka Kasa fasawa.
Amma da Manzon Allah (saww) ya dauki abin tonon, ya daki dutsen nan sau Uku sai gashi dutsen ya rududduge kamar gari!!
Aranar yakin Hunainu, lokacin da idanuwan jarumai sukayi Ja-jawur, Wahala ta kai wahala, kowa yana gudu daga wajen Yakin amma shi Manzon Allah (saww) sai Qara kutsawa yake yi!
Yana kirari yana cewa : "NINE ANNABIN BA QARYA BANE, NINE 'DAN ABDULMUTTALIBI!!!".
Ya Allah yi Salati da tasleemi bisa Annabinka mai Qarfi da Qarfin Qudura, wa alihi wa Sahbih.
Albarkacin wannan Salatin ka tabbatar damu acikin Manyan Masoyansa, ka azurtamu da kaunarsa da yin biyayya gareshi, biyayya ta gaskiya.