TAMBAYA TA 1624
*******************
Assalamu alaikum, mallam gaisuwa da fatan alkhairi. Mallam mene ne tabbacin wannan kissar "wata mata da tazo wajen Annabi Musa (AS) cewar tayi zina ta haihu kuma ta kashe dan, sai yakoreta sai aka aiko mala'ika Jibril ya gaya mai cewar laifin masu barin sallah da gangan yafi abun da ta aikata????
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Tabbas nima naga wannan Qissar acikin KITABUL KABA'IR na Imamuz Zahabiy (rah) acikin babin da yake magana akan laifin wadanda suke wulakantar da sallah.
Na san dai Imamuz Zahabiy babban Malamin hadisi ne. Kuma ba zai dauko abu marar tushe ya sanya acikin littafin nan nasa ba.
Bisa yadda Qissar take, wato tana daga cikin Isra'iliyyat. irin Qissoshin da aka samo daga hannun Malaman Yahudawa wadanda suka musulunta. Manzon Allah (saww) yace kar mu gaskatasu kuma kar mu Qaryatasu. Mutukar dai abinda yake cikin Qissar bai ci karo da Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww) ba.
Qissar tana nan mun kawota acikin Karatun Kitabul Kaba'ir wanda muke gabatarwa a ZAUREN FIQHU