Assalamu alaikum.
Don Allah malam a taimaka min da amsar wannan tambayar kamar haka:
Ko Qur'ani da hadisi sunyi Magana akan halaccin kaciyar mata, ko kuma wani daga cikin magabata na kwarai yayi Magana akan haka ???
(Daga Maryam Saleh)
AMSA.
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To 'yar uwa akwai hadisai da sukazo akan cewa:
Mustahabbi ne, yin kaciyar mata, saidai anyi sabani akan ingancinsu.
Wasu malaman sun raunana su, wasu kuma sun inganta su.
1. Baihaqee a Sunanu Assugrah hadisi mai lamba ta: 3712.
Ya rawaito mustabbacin yin kaciyar mata daga Ibnu Abbas da sanadi mai kyau.
2. Hadisin da Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a lamba ta: 108.
Daga uwarmu Nana A'isha tana cewa:
"Idan kaciya ta hadu da kaciya, to wanka ya wajaba"
Kaga wannan yana nuna cewa:
Sunnah ce yiwa mata kaciya a zamanin Annabi (s.a.w) amma ba wajibi bace.
3. Ibnu- Abi-zaid Al-kairawany ya ambata a Risala shafi na: 410 cewa:
Yin kaciyar mata mustahabbi ne.
Nasan wadansu zasuyi tambaya akan cewa:
Menene amfanin yin kaciya ga mata ???
AMSA.
---------
Yiwa mata kaciya yana karesu daga cututtuka da alfasha.
Saboda tana rage kaifin sha'awa ga macen da bata da aure.
wacce aka yiwa kaciya tafi samun Ni'ima ajikinta da kuma tsaftar al'aurarta.
Amma Wacce ba'a yiwa kaciyar ba, takan samu cututtuka kamar ìrinsu.
1. Warin al'aura.
2. Fitowar Qari dadai sauransu.
Domin neman Qarin bayani sai aduba Al-mugni 1\101.
Allah shine mafi sani.