TAMBAYA TA 1618
********************
Assalamu alaikum malam gidammu muna da yaro mai suna MUHAMMAD to mal. ba laifi ko na kirashi da wannan babban sunan ??
(Daga Yahuza Abdullahi).
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Eh ya halatta ka kirashi da wannan sunan. Amma ka sanya Qauna da girmamawa duk lokacin da zaka ambaceshi.
Manzon Allah (saww) yace:
"IDAN KUKA SANYA MA YARO SUNA MUHAMMAD, TO KU GIRMAMASHI, KUMA KU YALWATA MASA AWAJEN ZAMA. KUMA KAR KU CI MUTUNCINSA, KAR KU BAKANTA MASA FUSKA".
(Imamul Hakim ne ya ruwaito hadisin).
Don haka ba daidai bane ka ambaci sunan yaron ka zageshi, ko kuma ka gaya masa wata bakar magana.
Akwai falala mai yawa cikin sanya ma yaronka suna MUHAMMAD. Amma wajibi sai an sanya ladabi da girmamawa wajen Mu'amala da shi kansa yaron.
WALLAHU A'ALAM.