TAMBAYA TA 1637
********************
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Ina fata malam da iyalansa sun tashi lfy. Ya ibada? Allah yasa mu dace da falala, rahama da albarkan dake cikin watan. Allah yasa muna daga cikin wa 'yanda za'a 'yanta daga wuta. Ameen. Dan Allah malam tambaya ce dani yanzu nayi wannan mafarkin saduwan shine nakeso insan ya matsayin azumina? But banga wani discharge ba. Nagode Jazak'Allahu khair.
(daga wata Baiwar Allah).
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Magana mafi inganci ita ce Idan mai azumi yayi/tayi mafarkin saduwa, to azuminsu bai karye ba.
Azuminsu yana nan. Kuma ba zasuyi wanka ba sai dai idan sunga maniyyi ya fita ajikinsu azahiri. Idan mutum ya farka ya duba jikinsa yaga babu abinda ya fita, to ba zaiyi wanka ba.
WALLAHU A'ALAM.