Manzon Allah s.a.w yace Abubuwa guda hudu idan suka kasance akan mutum musulmi, babu abunda zai gagaresa A duniya ↓↓
1 - Riqon Amana (kamewa da cin amanar Dukkanin mutane musulmine ko kafuri)
2 - Fadin gaskiya (kamewa daga yasassun magangane da basu dace da shari'a ba)
3 - kyakykyawar mu'amala (kyautata xaman takewa tsakanin mutane
4 - Takaitawa wurin cin abunci (cin madaidaicin abun sha ko ci)
→Abuhuraira R.a
(muslum-bukhari)
FA'IDOJIN HADITH
→Riqon Amana xai jawo maka, yarda tsakanin mutane da amuncewarsu.
→Fadin gaskiya xai jawo maka daukaka da gaskata a wurin mutane
→Kyakykyawar mu'amala xata jawo maka so da kauna da son zama da kai da girmamawa awurin mutane.
→Takaitawa wurin da'amu, xai baka damar jindadin al'amurran rayuwa, yawan ci na kawo cututtuka mar yadda ya iganta daga manxon tsira.
→Aikata wadannan Abubuwa xai iya sana diyar musulunta ko shiryuwar wani.
ALLAH YASA MU DACE...
Admin M. Kabiru Muhammad