Wasu fulanine su ukushigo birnisai suka ga ana wasa da birisuka tsaya suna kalloakace biri yayi tafiyar Karuwa taga mai kudiBiri yai far da ido yana tafiya yana yanga da kwarkwasa kai kace wata tsohuwar karuwasanya shi yana kwaikwayon abubuwa daban daban yana
yi aka ce yayi tsallen kwadosai yayi sai Dan fulani yaji haushin biri yace yau ga shege. Sai akace biri yi zaman Dan fulani shanu sun kare sai biri ya dauko sandaya sa a kafadar shi ya lankwashe kafarsa Ya murtuke fuskaya zare idoya langabe kai jikin sanda, Dan fulani na ganin haka ya bushe da dariya ha ha ha ha haya ce
"Kwal uba Aradu kamar Baffa!!!"