QUL HUWALLAHU (wato Suratul Ikhlas) surah ce wacce babu irinta duk cikin Alqur'ani mai girma. Saboda abubuwan da ta tattaro na tauheedi da tsarkakewa ga Ubangiji.
Don haka ne ma Manzon Allah (saww) ya fadi falalarta acikin hadisai masu yawa.
Manzon Allah (saww) yace ma wani Sahabinsa mai suna Uqbah. "YA UQBATU, SHIN BANA SANAR DAKAI WASU SURORI BA, WADANDA BA'A TA'BA SAUKAR DA IRINSU ACIKIN ATTAURA KO ZABURA, KO INJEELA BA.
KODA ACIKIN ALQUR'ANI BABU KAMARSU. KAR WATA RANA TAZO MAKA FACHE SAI KA KARANTASU ACIKINTA.
SUNE: QUL HUWALLAHU, DA QUL A'UDHU BIRABBIL FALAQ, DA QUL A'UDHU BIRABBIN NAAS".
Aduba cikin Silsilatul Ahadeeth As-Saheehah. Hadisi na 2,861.
2. Abu Hurairah (rta) yace: "Mun taho tare da Manzon Allah (saww) sai yaji wani mutum yana karanta Qul-Huwallahu ahad. Sai yace "TA WAJABTA".
Sai nace "Mecece ta Wajabta"
Sai yace "ALJANNAH".
(Tirmiziy ne ya ruwaito hadisin akan lamba ta 2320).
3. Daga Mu'az bn Abdillahi bn Khubayb, daga Babansa (ra) yace:
"Mun fita cikin wani dare wanda akayi ruwan sama, muna neman Annabi (saww) domin yazo yayi mana sallah.
Da na riskeshi sai yace mun "FADI". sai nayi shuru. Sai ya sake ce mun "FADI" sai nace "MAI ZAN FADA YA RASULALLAHI".
Sai yace min "QUL HUWALLAHU AHAD DA FALAQI DA NAASI. KA RIKA FA'DARSU DA YAMMA DA SAFE. SUN ISAR MAKA DAGA KOWANNE SHARRI".
Tirmizy ne ya ruwaito.
ZAUREN FIQHU yana kira ga iyayen yara cewa mu rika yawan karanta ma yaranmu Qul huwallahu da Falaki da naasi domin nema musu tsari daga kowanne sharri.
Hakanan idan yaro yana firgita ko kuma ba ya yin barci sosai, ko kuma idan yana fama da ciwon kai, ko ciwon ciki, arika tofa masa wadannan surori masu albarka. in sha Allah zai samu lafiya da izinin Allah.