A Najeriya, hukumomi a kasar sun tabbatar da mutuwar mutane da dama, sannan wasu kuma suka samu raunuka sakamakon harin kunar bakin wake a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Harin ya aukune a kofar babbar kasuwar Jimeta bayan an fito sallar Magriba a ranar Alhamis, a daidai lokacin da 'yan kasuwar suka rufe shaguna da rumfunan su.
A jihar Borno ma, rahotanni sun ce wani dan kunar bakin waken ya kai hari a wani wurin binciken ababen hawa, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wasu mutane.
Jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA, Alhaji Muhammad Kanar ya ce mutane da dama sun mutu a harin na Yola, sananna ana yi wa wasu magani a asibitoci.
A baya dai, ana danganta irin wannan hari da ayyukan kungiyar Boko Haram.
Masu kai hare haren sun zafafa tun bayan da sabon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha alwashin daukan tsauraran matakan murkushe kungiyar Boko Haram.
Title :
Dan kunar bakin wake ya halaka mutane a Yola
Description : A Najeriya, hukumomi a kasar sun tabbatar da mutuwar mutane da dama, sannan wasu kuma suka samu raunuka sakamakon harin kunar bakin wake a Y...
Rating :
5