Ummah tana asibiti ita da salmah nikuma ina
gida ana zuwa yimin gaisuwa gidanmu yacika
sosai ina zaune ina tunanin irin soyyayyar da
daddy yake nuna min kafin yarasu' ina cikin
tunanin ne salmah ta kira wayata' nadaga nace
hello! Tace yaya ummah ta samu sauki amma
sunce sai gove zamu dawo' ok na kashe wayar'
sammah ya kalleni yace kb gsky kayi rashi' nace
Hmm hakane amma kada kamanta fa yanzu
natashi daga dan Alhaji na dawo nine Alhajin'
hamza yace gaskiyane kb yanzu sai abinda
mukaga dama kenan' nace ai kubari ayi sadakar
bakwai kowa mota zan bashi' su daddy suka dau
shewa dan murna' jama'a kuwa suka juyo suna
kallonmu suna mamaki saidai ba wanda zai iya
yimin magana'
Andawo da ummah gida saidai likita yayimana
bayani akan kada asake adinga bata mata rai'
ummah ta kirawomu ta zaunar damu nida
salmah' tace kabir abinda yasa na kirawo ka
inaso nasanar dakai cewa mahaifinka yarasu
yabar dukiya mai yawa dan haka yanzu komai zai
koma hannun ka dan haka yazama dole duk
shashancin da kakeyi ka daina' ke kuma salmah
alokacin da mahaifinki yarasu bakida wayo yabar
miki kudi da kadarori alhajine ya saida kadarorin
yazuba kudin abanki gaba daya' yana jiran ki
kammala degreen ki ya damka miki dukiyarki sai
kuma gashi Allah yayi masa rasuwa' dan haka
yanzu kudinki sun zama naki ke kikasan yadda
zakiyi dasu' domin ni ina ji ajikina kamar bazan
dade aduniyar nan ba' salmah tace haba ummah
kidaina cewa haka dan Allah bamu dawani gata
saike' ummah tace kabir kayi shiru? Nace ummah
me zance ai inajinku' na tashi na fita
abokaina hamza sammah abdul daddy kowa
sabuwar mota na se masa nan fa namanta da
komai an dawo clubbing sosai bani da aiki nan fa
na dinga cin dukiya kamar bazasu kareba'
ummah tayi tayi dani akan naci gaba da juya
kudinnan amma ina sam nakijinta sai facaka nake
da kudi' ranar lahadi muna tsaye naji ankira ni da
sabuwar number' na daga nace hello! Naji
macece akace kabeer yakake? Nace lpy amma
wace? Akace Hmm rukhy ce' nace sai kuma me?
Tace kb inasan magana dakai' nace kisamu wani
kuyi maganar dashi inaga zaifi nakashe wayata'
hamza yace wace? Nace wata fool ce manta da
ita kawai
Su daddy rukayya hamza sammah da abdul suna
zaune' hamza yace kunsan fa raba kabeer da kudi
ba wani abu bane mai wahala' daddy yace haba
hamza ya zakace haka bayan kasan cewa masu
kudi sunfi kowa son kudi' hamza yace ai shi
kabeer bai san waharlasu ba shiyasa' sammah
yace wannan gaskiyane' abdul ya kalli rukhy yace
ke duk wani abu yana hannunki domin ke kadai
ce zaki iya ansomana dukiyar nan' rukhy tayi
dariya tace ai baku da matsala indai nice wayarta
kawai mu hadu dashi face 2 face' suka sheqe da
dariyar mugunta' suka watse' ni abinda
bansaniba shine ashe su hamza niyarsu kawai ta
su damfareni ce' nikuma gaba daya na saki jiki
dasu'
Ina zaune a falo salmah ta shigo agigice tacemin
yaya jikin ummah ya tashi na tashi da sauri muka
shiga dakin' muka tarar da hajiya tana aman jini
agigice muka daukota muka sata amota sai
asibiti likitoci suka tsaya akan hajiya' na tambayi
likitan nace doctor wai meyake damuntane? Yace
gaskiya fa da matsala domin kuwa zuciyarta ta
samu matsala dan haka gaskiya saidai ku fitar da
ita waje' nace yanzu wace qasa yakamata
akaita? Yace ba inda yafi dacewa a kaita sai
egypt' nan muka gama shiryawa akan cewa za'a
kai ummah egypt ranar litinin sukuma asibitin
zasuci gaba da kulada ita kafin ranar' salmah
kuka kawai take tace yaya yanzu dole sai ranar
litinin za'a kaita? Nace amma ai kinaji dai suka
fada dai' salmah ta zauna zata kwana awajen
ummah ni kuma na koma gida na shirya muka
tapi club domin ranar akwai chillimg dan anan
ma zamu kwana'
Misalin karfe uku na dare muna cikin club wayata
tafara ringtone ina dubawa naga salmah ce take
kirana nayi tsaki nabarta taci gaba da ringtone
sai salmah ta kirani x16 amma naki picking' da
naga dai ta dameni kawai sai na kashe wayar
naci gaba da abinda nake' wata tsaleliyar yarinya
tazo inda nake tace sannu fa' nace yauwa' tace
rukhy' nace oh! Bansan ke bace da bazan kashe
miki wayaba' ta ce Hmm kb kenan kasan wani
abu kuwa? Nace a'a sai kin fada' tace ka dade
kana burgeni amma sai naji wakar birthday dinka
tare da wata salmah to sai nayi tunanin girlfriend
dinka ce amma daga baya sai naji ashe kanwarka
ce' nadanyi dariya nace haba yaza'ai nayi
soyayya da wannan yarinyar ai na girmi ajinta'
nandai soyyaya ta kullu a tsakanina da rukhy
domin kyawun da rukhy take dashi shine abinda
ya rudeni' su hamza kuwa suna gefe suna
kallonmu'
Misalin karfe 7:30am nadawo gida ina zuwa na
tarar da jama'a jingim a kofar gidanmu' nakarasa
da sauri nace lpy? Naga kowa yayi shiru da sauri
na shiga gida domin naga abinda ke faruwa' YA
SALAM! Shikenan nida salmah munzama daya
domin kuwa ina shiga natarar ana yiwa gawar
umma wanka' natsaya cak! Numfashina ya dauke
jiri yafara dibata dan dole nadafa gini na fara
wani kuka wanda bantaba yin irinsa ba duk
wanda yake waje saida ya tausayamin salmah
itama kuka kawai take ta taso tazo inda nake
tace yaya kayi hakuri dan Allah kukan ka yana
qara karyarmin da zuciya na kalleta naci gaba da
kukana' aka gama shirya ummah sai makabarta
ina gani aka saka ummah aka rufe wani sabon
kuka nafara yi' mutane suna juyawa amma ni
sam naki tashi na zauna dakyar aka janye ni'
shikenan nima nazama maraya ba hajiya ba
Alhaji azuciyata nace Allah sarki ashe haka
salmah takeji azuciyarta'
Wata daya da rasuwar ummah dagani sai salmah
a gida kullum sai salmah ta kawo min abinci
amma sam banaci' kullum wulakancin danake
yiwa salmah kara yawa yake
Amma ita kuwa bata gani' soyyayarmu da rukhy
tayi karfi sosai sabuwar mota na sai mata
watarana muna tare da rukhy tace kabeer gsky
inada magana dakai' nace menene? Tace gsky ni
idan kanason muci gaba da soyayyarmu dolene
ka karabuda yarinyar nan' kasanfa mutane suna
zarginku' nace ni kaina na fara tunanin hakan'
kada ki damu zan san yadda zanyi da ita
Ina dawowa gida na kwalawa salmah kira tazo
nace yawwa inason nafada miki yau dinnan ki
tattara kayanki ki koma gidanmu na zoo road dan
bazai yiwu muzauna agida daya ba' salmah tace
haba yaya yanzu baka tunanin zamana ni kadai
acan akwai matsala? Nace ke nifa nagama
magana dan haka da yamma kada nasameki
anan' najuya na fita
Allah sarki ina dawowa na tarar salmah ta
kwashe kayanta kaf! Ta bar gidan' ina dubawa
kan gadona naga letter nadauka nafara
karantawa kamar haka:- Assalm alaika yayana na
soka matuka amma kai kuma ka tsaneni bansan
meyasa ba kace na bar gidan da kake nakoma
wani' to kasani na barma garinma ba gidan ba
nima zanje na gina rayuwata amma dai kasani
inasonka har abada daga kanwarka kuma
masoyiyarka salmah.......wani irin hawaye ya
zubo daga idanuna' da sauri na fito na dau mota
sai zoo road ina zuwa na tarar da gidan arufe
yanda yake na kira wayar salmah akashe.........
.... Muhadu a part5