A sharaton hotel na sauka' ina shiga america
nasan cewa lallai sun tserewa kasashenmu na
africa ta fannoni da dama' nashiga nayi wanka
na ci abinci tuni bacci yadaukeni' ban tashiba sai
da yamma nafito waje sai wajen bude idanu
tunda na fara yawo bandawo gida ba sai da dare
yayi sosai'
Acan gida nigeria kuwa Abba da hajiya da salmah
ne zaune a darling table zasuyi break fast' Alhaji
yace yaron nan fa nakira wayarsa amma taki
shiga salmah tace wallahi daddy nima nayi ta
kira amma baya shiga' Alhaji yayi murmushi yace
hajiya yar nan taki kodai yar gida za'ayine?
Hajiya tace Alhaji ashe kaima dai ka ganeta'
salmah ta rufe fuska tayi waje tana dariya daddy
ya cewa hajiya kinganta wai ita mai kunya'
hajiya tace Alhaji yarinyar nanfa ba karamin son
kabir take ba amma shikuma ya dauki tsanar
duniya ya dora mata kai kuma bakasan laifin
yaron nan ko kadan' Alhaji yace hmm hajiya
kenan' kinga ni bari ma nasake gwada wayarsa'
Ina cikin club duk inda na juya turawa nake gani
sai chilling ake yanayi clubbing dinmu da nasu da
banbanci yammata ne zaka gansu kusan tsirara
suke duk da wannan itace irin rayuwar danakeso
amma fa abin yayi muni matuka' tuni nasamu
wata yarinya moniter ta zama girlfriend dina'
rayuwata ta canza gaba daya sai kace ba
bahaushe ba haka naketa abubuwana a america'
yau saura kwana biyar na dawo amma jinake
kamar asake karamin shekaru acan domin
nasamu irin life din danakeso'
Ina zaune wayata ta fara ringtone inadubawa
abba na gani cikin murna na daga nace haba
daddy tunda nazo nayi try din numberka amma
yaki shiga kai kuma baka kirani ba gsky ni nayi
fushi ' daddy yace sowie my son kasan bazanki
kiranka ba' nace to daddy ina ummah na? Yace
kasan yanzu bana gida saidai idan nakoma'
daddy yace ina fatan kanajin dadin kasar ko?
Nace daddy sosaima' yace amma dai kasan
sauraa ranar monday jirginku zai taso ko? Nace
eh daddy' yace yauwa my son kana dawowa zan
shirya maka birthday' nace wow! Daddy na ina
sonka' yace m2 my son' muna gama waya da
daddy ne naga wani kiran da sabuwar number
nayi picking nace hello! Inajin muryar nasan
salmah ce nace ke lapiya? Salmah tadanyi smile
tace haba yayana kenan meyasa kullum kake
nuna kiyayyarka a gareni ne? Nace wallahi da ina
kusa dake sai nayi ball dake ni zaki dinga yiwa
wannan tambayar mtsw! Tayi dariya tace yaya
kenan wai yaushe zaka canzane? Nace
bansaniba na kashe wayata' a zuciyata nace wai
salmah me take nufi dani ne? Kodai sona take?
Meyasa zatasoni bayan tasan na natsane ta?
Tambayoyin dana kasa baiwa kaina amsa kenan'
Misalin uku na yamma jirginmu ya sauka a gida
nigeria su su ummah da salmah ne sukazo
daukata salmah tana ganina sai murmushi ni
kuwa na hade rai' ta karaso da sauri tace yayana
sannu da zuwa' ko kallonta banyi ba nace toh'
ummah tace Hmm ai wannan yayan naki bazai
canza ba' nace umma ina daddy? Tace ayyah!
Yau yana da meeting kaduna shiyasa ya turo mu
muda driver' nace ok nashiga mota salmah
tashigo ta zauna kusa da sit dina'
Washe gari da sape daddy ya dawo muna zaune
a darling table daddy ya kalli salmah yace
yayanki dai yadawo sai kidaina damunmu' tayi
dariya nikuma na bata rai nace daddy nifa banaso
adinga hadani da wannnan yariyar' ummah tace
kaidai shashashane mutum da yar uwarsa amma
yana gudunta' daddy yace yauwa my son nagama
shirya birthday dinka ranar litinin mai zuwa nace
yauwa daddy naji dadi' salmah ta sauri tace lah!
Yaya zan gayyato kawayena' na kalleta nace ke
wlh kada ki sake inga wasu banzayen yara
awajennan na fadamiki' daddy yace a'a my son
kabarsu suzo kaji? Nace a'a gaskiya daddy'
daddy yace to shikenan dama nayi maka order
sabuwar mota amma nafasa tunda hakane' nace
lah! Daddy na yadda wallahi ta gayyato su'
ummah tace ai itama zata yanka cake' salmah
taji dadin bayaninsu daddy nikuwa araina banso
hakanba dandai kawai ina son hawa sabuwar
motane saboda in nuna wa su riyaamah da
maryam da fatima ni ba sa'ansu bane'
Ranar litinin waje ya tsaru yayi kyau sosai wajen
parking din motoci yacika manyan yara ne
awajen yayan manya maza da mata' farar suit
dita nasa dana taho da ita daga america' salmah
ma fararen kaya tasa hakan ya batamin rai sosai'
nan dai aka fara abinda ya taramu' magabatarwa
ya mike yace akwai mawaki wanda zaiyi wakar
birthday wanda kanwar kabir tasashi yayi wato
salmah' nan mawakin ya mike yafara wakar waka
tayi sosai saidai yanda me wakar yabayyana
salmah amatsayin masoyiyata yayi matukar
batamin rai sosai haka kawayen salmah suka
dunga zuwa munayi photo' itama salmah munyi
pic nida ita dayawa' badon ina ganin idon mutane
ba da hakan bazai yiwu ba' nan dai akagama
muka bar wajen nida abokaina'
Misalin karfe takwas daddy ya taramu yacemana
yanzunnan zantafi jigawa tafiya ta kamani amma
yau zan dawo dan haka kabeer sai ka kula domin
komai ya dawo hannunka nace daddy ba matsala'
muka raka daddy nida salmah' bayan amma ya
tafi muka shigo mota muna tafiya salmah ta
kalleni tace yayana dan rakani shoprite mana
zanyi shopping' nadan kalleta nayi murmushi'
salmah tayi matukar yanda nayi mata murmushi
abinda ban taba yimata ba' nace wai dan Allah
meyasa baki da zuciya ne? Tace yaya meyasa
zanyi zuciya da abinda nakeso? Cikin bacin rai
nataka brake na tsaya nace ke amma baki da
hankali ni zaki kalla kice kinaso? dama bakisan
inajin haushinki kinsa anyimin wakar birthday
ansa sunanki wai ke ga masoyiyata ko? Tace
yayana wallahi duk sanda kayimin wulakanci
maimakon naji haushi sai sonka yakara karuwa
acikin raina...... Na daka mata tsawa nace dallah
fita daga motar nan' tace haba yaya na daka
mata tsawa agigice ta fice naja mota na barta
anan'
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN yamma
tayi ina shirin fita club wasu motoci sukayi
parking akofar suka shigo wayyo! Allah na ni
KABEER gawar daddy aka shigo da ita yayi
accidient a hanya ya rasu tuni gidan ya dauki
koke-koke tuni hajiya ta yanke jiki ta fadi sai
asibiti nikuwa na rude sai jijjiga daddy nake ina
kuka salmah ma kuka take tana janye ni tana
cewa yaya kayi hakuri ka tashi nikuwa kuka
kawai nake.......