Tuni ta fara ja baya tana fadin (la ila ha illa anta
subhanaka inni kuntu minazzalimin) tuni nasa
hannu na fesa mata mari nace ni kk wa addu'ah?
Nakara matsawa inda take ta riga ta kure daga
ita sai bango dan dole ta tsaya naje dab da ita
ina iya jin numfashinta na kalleta hakika salma
kyakykyawace matsalar kawai ni kallon yar aiki
nake mata' tuni salma tagama tsorata da abinda
nake shirin aikatawa' nace ke mahaukaciya me
kike tunanin zanyi miki? Dama koda baki shigo ba
ina da niyar samunki nayi miki warning' shine
zakije skul dinku kidinga ce musu wai ke yar
kanwar Alhajina ce ko? Tace wallahi a'a yaya
kabir wasune suka fada musu baniba' na daka
mata tsawa nace ke wawa idan bake kika fada ba
wane zai san alakarmu dake? Dan haka inaso ja
kunnanki wallahi duk sanda kika sake fadar wai
munada alaka sai nayi maganinki' kin manta
cewa ke mahaifanki sun mutu? Don haka ki dinga
daukar kanki a matsayi yar aiki saboda bazai
yiwu ace nida gidan ubana ace muzama daya da
wani ba' kuma duk abinda nakeso shi daddy yake
ita kuma hajiya bazata iya tsallake umarnin
daddy ba dan haka wallahi idan kika ci gaba da
zubar min da class dina sai nasa kin koma inda
kika fito banza kawai fitarmin daga daki' da sauri
tabar dakin dan dama atsorace take'
1:00am yayi dadai da lokacin motocin sukai
parking a harabar club muka fito gayu suka biyo
bayana' shigar mu keda wuya salon clubing ya
canza na fara hada dancing competetion' ina
saka kudu kamar dubu dari' ana cikin haka kudin
wajena suka kare' nace daddy!! Ya amsa da sauri
nakalli sammah night driver na nace bashi key
din motar nan yabude boot akwai kudi ya debosu
duka' ya bashi daddy tafi ya kawo da sauri' mu
biyar mukaje wajEn sammah abokina ne amma
idan dare yayi shine yake min driving sai hamza
abdul daddy auwal wadanda suke bina kullum
dan aji dadin rayuwa' ana kiran sallar asuba
muka dauki hanyar gida'
Tunda na dawo na shiga bangarena na kulle na
kashe wayoyina saboda nasan hajiya zata tasheni
ban tashiba sai karpe uku na yamma nayi wanka
na kwalawa salmah kira ta kawo min abinci' ina
gama ci hajiya tazo ta fara tambayata ina kaje
jiya? Nace hajiya naje walima ne dare yayimin
shine na kwana acan' hajiya tace kabiru meyasa
kake so kadinga batamin rai ne? Nace haba
hajiya nifa nace miki banaso kidinga cemin kabiru
sai kace wani dan kauye ni kabeer nafi so' hajiya
ta kalleni cikin bakin ciki tace gaskiya yaron nan
kayi nisa amma ina rokon Allah ya shiryaka' na
tashi nayo waje cikin fushi nasamu nura mai gadi
nace kai meyasa kakeyimin shaida wajen hajiya?
Nura ya mike a tsorace dan yasan halina yace
wallahi banyi maka shedar komai ba' na daka
masa tsawa nace dallah can yimin shiru idan
bakaiba wane yasan karpe nawa nake fita karfe
nawa nake dawowa? Ku dama talakawa da an
kawo ku cin arziqi saikun nuna halinku' nura yace
wallahi ni ban fadamata ba kabiru.......tas! Karar
marin dana sheka masa shiyasa shi dakatawa
tare da dafe kumatunsa' nace kai ni zakacewa
kabiru an fada maka nima bagidaje ne irinka'
yace kayi hakuri dan Alhaji wallahi mantawa nayi'
na juya na bude mota na fita.
Muna zaune nida friends dina sunata labaransu
nikuma ina chatting kawai sai wani guy yayi
pArking a mota cikin bacin rai yazo gabana yafara
masipa yana cewa kai dan Alhaji kake ko wa?
Abinda kake ya isheka haka meyasa dan kanwata
ta kalleka zaka mareta? Hamza yace an mareta
meza kai? Yace kai dan karere ba dakai nake ba'
daddy ya mike a fusace zasuyi fada nacewa daddy kyaleshi' na kalleshi nace ka gama? yace eh! Nace to jeka ya juya yana tunanin na kyaleshi' tuni nazaro piston din daddy na dana
dauka bai sani ba na harbeshi a cinya' nan ya fadi yana ihu mukuwa mukai sauri muka bar
wajen' Ina gida Abba ya kwalamin kira' ina zuwa yace haba my son meyasa kadauki gun dina? Nayishiru' yace yanxu gashi ka harbi yaron mutane sukuma kasan mutane ba hakuri garesu ba gashi
yanzu har sunkai kara court' nace daddy to ai kai kasan yadda zakai dasu' daddy yace yanxu gobe
gobennan zaka bar kasar nan zakaje america kayi two weeks idan angam a sai ka dawo' nace kai
amma daddy naji dadi ni wannan abinma gaba takaini'Tuni nasamu friends dina nafada musu aka hadashow (party) mai zapi na murnar tafiyata america nabi gayuna da 200,000 kowa na dawo gida inatunanin abinda zanyi idan naje america' ina zaune salmah tayi sallama ko kallanta banyi ba'
tace yaya kabeer hutawa kake? Nace a'a gudunake tunda ke makauniyace' ta danyi murmushi
nikaina nasan salma kyakykyawa ce amma sai dai girman kaina bazai bar zuciyata ta yabeta ba'
salmah tace yaya yanzu gobe tafiya zakai kabarmu? Na daka mata tsawa nace ke dallah
tashi kibar dakinnan' a firgice salmah tabar dakin tana tafiya tana juyowa'Muna cikin club ne wayata tafara ringtone inadubawa naga alhajina ne na daga nace hello!daddy' Yace my son kayi sauri ka dawo gida visa ka ta america ta zama ready' na wayyo daddy inasonka' alhaji yace kayi sauri fa kasan ka harbi yaron mutane jama'a sunzo nan sun tarar min
wai sai anbi musu hakkinsu dakyar nasa aka
watsa su dan haka kazo katafi yanzunnan' nace
to daddy' nan take na hado kan gayuna nace
musu kufa adaren nan jirginmu zai tashi sukai
min murna sosai'
Nagama shirya komai abokaina da yangidanmu
duk sunyo min rakiya zuwa airport' kowa yana ta
cewa Allah ya kiyaye' nidai na kagu nabar nigeria
domin nasan acan ne zanyi rayuwar danake so'
salmah ta matso inda nake tace yayana yanzu
sai yaushe ? Na kalleta nace ke dallah kada
kidameni' tadanyi murmushi mai kama da yake'
tace to Allah yakiyaye hanya' ko kallon inda take
banyi ba' hajiya tace dan Allah kabir idan anje
kada ayi shashanci nace haba hajiya nifa
banason fada wallahi' Alhaji sowie my son kasan
halin umman taka' nan jirgin mu ya tashi Alhaji
har kuka yayi saboda zai rabudani' sukuwa
friends dina haushinsu daya sun rasa mai daukar
nauyinsu wajen chillinG...........muhadu a part3
gove