Misalin karfe 2:00am yayi daidai da lokacin danake cikin club anata chilling na kalli agogon hannu na' nan take nazaro key din mota ta nayo waje nahau kan titi na bude wine dita nafara sha' dare yayi tsit titi ba kowa nikUwa gudu kawai nake shararawa abunka da wanda yake a buge' daga nesa na
hango hasken fitila ana tsaidani' ko alamar tsayawa banyi ba saida na matso sai naga itace akan hanyar hakan ya tilasta min yin slow na dan tsaya' "yan sanda ne suka taso suna gani naji dayan yace kai dan Alhajine pa' sai suka janyemin itacen nikuwa ko kallonsu banyi ba' nasake canza gia haka naita kwarara gudu akan titi har na isa gida' megadi ya tashi a gigice yabude min gate' nasaka mota ta' na fito yAce dan Alhaji barka da zuwa ko kallonsa banyi ba' bangarena nayi na zube sai bacci duk yinin ranar banyi
wata sallah ba' Misalin karpe 12:00pm yayi dadai da lokacin dana tashi daga bacci nayi
wata mika tare da hamma' nayo bandaki nayi wanka nayi brush na nupi (darling table) ina zuwa na tarar bakomai akai na kwalawa salma kira ta taho da sauri' tana zuwa nace ke mahaukaciyar ina ce bakisan sapiya tayi bane ? baki ajemin abinci ba' tafara magana a tsorace tace na aje wallahi
hajiya ce tace na dauke dataga rana tayi' na kalli agogo naga 12:20pm cikina kuwa qugin yunwa kawai yake' nadaga hannu na zabga mata mari nace amma kedai wawace wallahi' tayi
wata kara dan zapin marin' hakan yasa hajiya tayo kasa tana zuwa ta tarar dani ina masifa ita kuwA salma tana kuka' hajiya ta daka min tsawa' tacekai wane irin yaro ne wai? dan nasa
tadauke abincin shine zaka mareta?Meyasa kaje shegen yawonka har kakai dare kazo kana ta bacci har yanzu? To wallahi idan ka kara dukan yarinyar nan sai ranka yayi
mummunan baci........ Alhajine yakatseta yace haba hajiya meyasa kike yiwa danki na cikinki hakane
bayan kinsan yaron nan shi kadai garemu gaskiya kidaina yiwa yaron nan tsawa idan baso kike raina ya baci ba' Alhaji yajawo ni jikinsa yace yihakuri kaji dan auta na' nace dad ni wallahi ummah duk ta tsaneni komai nai sai tayi ta yimin fada agaban wadannan banzayen mutanen' alhaji yace am sowie my son' nace abba nifa banyi breakfast ba' abba yace haba hajiya meyasa kk barin yaron nan da
yunwa? Hajiya tace alhaji wannan yaron pa yawon dare yake zuwa idan baka saniba gara ma kasani' alhaji yace in banda abinki shikenan yaro bazaije yawo ba haba hajiya wai idan dana
baiji dadin arzikina ba wane zaiji? ummah tace gaskiya Alhaji wannan ba gata bane' dad ya rike hannuna yace my son muje restaurant kayi break nace to dad' mukai waje ummah tabimu da kallo' Ummah tace salamah kinga ke marainiyyace kuma mahaifiyarki kanwar Alhajice amma duk da haka
bai hana yaron nan yimiki wulakanci ba shikuma Alhaji soyayyar dayake yimasa tahanashi yadinga tsawatar masa' salmah tace ummah ai ni nasan insha Allahu watarana yaya kabir zai
daina' ummah tace to ya maganar soyyyar taku kuma? Salmah ta sunkuyar dakai tana dariya tace
ummah ai shi yaya kabir baisan ma ina sonsa ba' ummah tace mezai hana ki fada masa? Salmah tace ummah ai tsoronsa nake' ummah ai wannan yaron bansan inda ya dakko wannan mugun halinba amma ki kwantar da hankalinki insha Allahu zai nutsu' salmah tace Allah yasa ummah' Misalin karpe 11:pm hamza yakira wayana nadaga nace hello! Yace dan Alhaji yau akwai hot chilling nace ok kuzo gida ku sameni saimu wuce yAce to shikenan' ina zaune a falo salma ta shigo rike da cup din shayi a hannun ta' na kalleta yarinyar kyakykyaWa ce matuka amma sai kash! Ni kallon Yar aiki nake yimata abinda zuciyata ta rayamin kenan' na daka mata tsawa nace ke lafiya? Tace naga kana zaune ne shine na kawo maka tea' nace ke dallah can nifa banason shishshigi kada ki kara yimin abu idan ban saki
ba' tace to' tajuya ta fita Ranar litinin ina zaune a bangarena ina kallon wakar eminem dagani sai
wando iya gwiwa sai singlet naji an turo kofa salma ce ta shigo ina kangadona ko motsawa banyi ba' agigice tace dan Allah kayi hakuri wallahi bansan kana ciki ba hajiyace tace nazo
nagyara maka daki' ta juya zata fita' nace ke ina zaki zonan! A tsorace ta dawo tana kyarma' nace bazaki zo nan ba? Ta kara matsowa a tsorace' na mike daga kan gadon nayo inda take gadan!! Gadan!!