Yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Niger da Chadi na tattauna yada za akawo karshen matsalar yayan boko haram alummar jihar Borno musammam ma cikin garin Maiduguri suna ci gaba da huskantar hare-haren daga wajen wadannan mahara dake kyautata zaton cewa yayan kungiyar boko haram ne.
Ko jiya sai da aka samu wani tashin bomb din a wajen binciken ababen hawa daf da kofar shiga barikin Maimalari wanda aka ce ya jikkata mutane da dama da kuma hallaka wasu, sai dai an samu rahotanni masu karo da juna yayin da ake cewa wannan bomb ya tashi ne a cikin wata mota Sharon wasu kuma na cewa ya tashi ne cikin motar itace, sai dai batun da ya tabbata shine an samu tashin bomb din kuma ya hallaka mutane da dama, harin da wasu ke cewa nay an kunar bakin wake ne da suke fafatawa da jamiaan dake cikin dajin sanbisa, sai duk da wannan arangamar da jamiaan sojan keyi a dajin wadannan maharani sukan yanki jiki su hada boma-boman da suke shigowa dashi cikin birnin Maiduguri, wannan dai shine karo na biyar ana samun tashin bomb a jere a duk wayewar garin ALLAH taala, na tambayi wasu da gidajen su ke kusa da inda ake binciken wadannanabin hawa inda bomb din ya tashi ga kuma abinda suka shaida mani ta wayar tarho.
‘’Abin ya faru Haruna’’
A matan Itace ne?
‘’A’a a ciki motar sharan ne’’
Da mutane ne a ciki ko yaya?
‘’A da mutane’’
A bakin ina ne?
‘’Daidai wani gidan mai’’
Inda suke chekin din nan?
‘’Gaba dasu ne kadan, har ya taba sojoji ma’’
Kai abin ba kyau a unguwar mu ne abin ya faru, gaba da gida kadan, sojoji ma sun mutu fa wallahi
Zasu kai nawa?
‘’Mutane 6’’
Koma menene dai wannan lamari akwai abin dubawa ganin yadda hukumomin tsaron ke bugun kirjin cewa suna samun nasara akan wadannan mahara amma wadannan mahara su samu kwanciyar hankali su kutsa birane su tada boma-bomai a duk inda suke so kama daga kasuwanni da masallatai da wuraren Sanaa akan wadanda basu ci ba basu sha ba ba tare da sanin dalilin yin hakan ba.
Title :
CI GABA DA KAI HARE-HAREN BOM A JIHAR BORNO
Description : Yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Niger da Chadi na tattauna yada za akawo karshen matsalar yayan boko haram alummar jihar ...
Rating :
5