Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya yi hawan daba na musamman na bikin cika shekara daya a mulki.
Daruruwan jama'a ne suka fito kallon Mai martaba Sarki a yayin hawan daba na musamman a kofar fadarsa.
Wasu zababbun hakimai ne suka marawa sarkin baya a hawan a inda ya kai ziyara gidan mai babban daki wurin mahaifiyarsa sannan ya zaga wasu sassan birnin
A cikin shagulgulan bikin har da tseren dawakai a filin sukuwa na Kano.