A wannan zamanin wannan muhimmin abu daya addabi mutane sosai, musamman matasa maza da mata shine SHA'AWA kusan kullum matasa na fadawa cikin bala’in fasikanci kala- kala a dalilin rashin sanin hanyar kaucewa haka.
Idan mutum yayi duba na tsanaki tareda la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani zaiga cewar dayawa wasu na fadawa cikin aikata fasiqanci ba cikin son ransuba, sai don abin ya fi karfinsu.
Sauda yawa zakaga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron ALLAH, yasan illar zina, yasan girman zunubin ta, amma saboda fitinar sha’awa yakasa daurewa yaje ya aikata din.
Wani haka zaita aikatawa yana tuba, da haka har zina tazame masa jiki ya runka ganin ai yinta ba komai bane. "SubhanAllah!"
Haka zakaga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, tasan illar zina, tasan girman zunubinta amma sai fitinar sha’awa tasa ta afka cikin wannan bala'i.
Domin kaucewa fadawa makarantar shaidan dole ne duk wani matashi dayake fuskantar barazanar Sha'awa ya yi la'akari da wasu dokoki da addini ya shar'anta masa, sannan kuma yayi amfani da dabaru wanda zasu taimaka masa.
Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya take, daga cikinta take bijirowa, don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awarsa duk lokacin da ta taso masa, sai yafara da gyara zuciyarsa tukunna.
Toya ake gyara zuciyar??
Ana gyara tane ta hanyar cikata da kyawawan tunani da shau’uka, da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta, da goge mazaunin duk wani mummunan shauqi.
Daga nan sai kyautata dabi’u halaye da ayyuka, duk wata dabi’a, wani hali ko wani aiki da mutum keyi indai bamai kyau bane, to yin watsi dashi zai kara haskaka masa zuciyarsa.
Kyawawan dabi’u sun hada da yawan murmushi, taimakawa ‘yan uwa, makwabta da abokai, gaskiya da rikon amana, da sauransu.
kyawawan ayyuka sun hada da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abinda akansa ba dai-dai bane a addinance sai ayi kokari a barshi komai dadinsa ko ribarsa.
Yawan sanya ALLAH a zuciya da yin zikiri.
ALLAH madaukakin sarki, Yafada cikin Alqur’ani mai girma cewa:
“Lallai da ambaton ALLAH ne zukata kan sami natsuwa.”
Jamar yadda In Qayyum take cewa "Da za'a Tarawa mazinaci 'yan matan duniya baki daya yayi zina dasu bayan ya gama sai a kawo wata budurwar guda daya wadda bai yi zinar da ita ba, sai sha'awar wannan matar (da aka kawo daga baya) ya kamashi.
Wa'iyazubillah...!
Shedan baya iya zama cikin zuciyar dake
ambaton ALLAH balle harya gudana cikin
hanyoyin jinin ta, to tayaya kuwa har zai
tafarfasar da fitinar sha’awar wannan zuciya??
Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yakewa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa.
Lallai ne 'yan uwa mu kula da kiyaye sallolin farilla da nafila da yawaita karatun al-qur'ani da sauran azkar dasuka tabbata daga manzon ALLAH sallalahu Alaiihi Wasallam.
Sannan dole mu kiyaye maganar Manzon ALLAH (s.a.w) inda yake cewa "yaku matasa duk wanda yake da hali ko iko toya gaggauta yin aure, wanda kuma bashida halin yin aure to yayi azumi domin wannan yana dakushe kaifin fitinar sha’awa".
Sannan dole su kansu Iyaye su kula da rayuwar 'ya 'yansu matasa maza da mata, domin karesu daga wannan bala'i.
Wani matashi ya taba tambayar wani malami cewa shi wallahi yana Azumi yana karatun Al-qur'ani Amma wallahi Sha'awarsa kullum karuwa take yi, malam yabashi amsa da cewa to lallai yadage yayi aure.
Kusan babban dalilin daya kan hana matasa aure shine rashin tsayayya ko kwakwkwarar sana'ar da mutum zai iya rike kansa da kuma Iyalinsa, wannan kam babban al'amari ne, domin babu yadda za'aji dadin aure idan babu wata hanya da mutum zai iya daukar dawainiyar iyalinsa.
Dan haka dole a dage a koyi sana'a domin a
dogara dakai.
Ya ALLAH ka baiwa dumbin matasan mu (maza da mata) dama da ikon yin aure albarkacin Rasulullah (S.AW).