An shawarci Shugan kasa, Muhammadu Buhari da ya janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke ba kamfanonin dillalan man fetur da sunan tana tallafa wa talakan kasar. Sakataren kungiyar dillalan mai ta kasa masu zaman kansu, ‘Indepent Petroluem Maketers Association of Nigeria (IPMAN),’ Alhaji Danladi Garba Fasali ne ya’yi wannan kira a lokacinda yake jawabi wa dimbin al’ummar musulmin da suka hallara a bikin kaddamar da asusun tallafa wa gasar karatun Alkur’ani mai girma, wanda kungiyar JIBWIS, reshen jihar Filato ta gudanar a Masallacin Jumma’a na ’Yan Taya Jos a makon da ya gabata.
Ya ce, karancin man Fetur da kasar nan ke fuskanta a yanzu ya biyo bayan dimbin bashin da kamfanonin dillalan man ke bin gwamnatin da ta shude, karkashin Dk. GoodLuck Ebele Jonathan ne.
Sakataren ya ci gaba da cewa, gwamanatin tarayya tana da Depots na mai sun kai arba’in a cikin kasar nan, amma duk ba sa aiki, wannan kuma ya kasance ne bisa wata manufa ta dabam. Ya ce su kananan dillalan man fetur da suke safaran mai din zuwa kowane lungu na kasar nan, ba sa samun mai din da sauki a hannun kamfanoni, su manyan dillalan ne da suke safarar man daga waje zuwa cikin kasar nan ke cin Karen su ba babbaka. Ya kara da cewa, irin wadannan dillalan suna da kananan Depot sun kai dubu Uku, inda suke sauke man kafin su sayar wa masu safarar man zuwa gidajen man da ke cikin kasar da farashi mai tsadar gaske. A irin wannan tsari ne gwamnatin tarayya ke kashe makudan kudade a kowace shekara.
Alhaji Danladi Fasali ya ci gaba da cewa yanzu waye yake ganin kalanzir a gidajen mai tun lokacin da aka rage farashinsa zuwa Naira Hamsin a kan kowace lita da sunan ana tallafa wa talaka? Ya ce rashin lura da irin wannan tsari da gwamantin da ta shude ne ya sa aka yi ta karkatar da kudaden talakan kasar nan, har ya kai ga yanzu ba abin da za a karkatar da shi din.
Ya kuma kawo shawarar cewa gyara matatun man kasar nan ne kawai hanyar da gwamanati za ta bi ta kawo karshen wannan matsala, kuma ta samar wa da dimbin matasa aikin yi. Ya ce, duk kasashen da ke makwabtaka da kasar nan, suna da matatun mansu, “amma sai ga shi mu da muke da man ba mu da matatar mai, a bisa wadansu dalilai na son kai,” in ji shi.
Tun farko a nasa jawabin, Shugaban majalisar Malamai ta kasa na kungiyar, Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, wanda mataimakinsa na biyu, Shaikh Sa’idu Hassan Jingir ya wakilce shi, ya bukaci al’ummar kasar nan da su ba sabon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da sauran Shugabannin da aka ransar da su cikakken hadin kai da goyon baya, don su jagoranci al’umma cikin nasara da sauke nauyin da aka dora masu. Ya ce, musamman Shugaban kasa yana bukatar addu’o’i daga wajen al’ummar don warware dimbin matsalolin da ya taras a kasa.
Title :
An Shawarci Shugaban Kasa Ya Janye Tallafin Man Fetur
Description : An shawarci Shugan kasa, Muhammadu Buhari da ya janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke ba kamfanonin dillalan man fetur da sunan t...
Rating :
5