Hukumar kula da safarar jiragen sama ta Najeriya ta ce ta sake bude filin jiragen saman Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Kakakin hukumar, Mr Yakubu Dati, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne bisa tabbacin da suka samu daga rundunar sojin kasar cewa babu wata matsala wajen zirga-zirgar jiragen sama a filin.
Ya kara da cewa tuni kamfanonin jiragen sama suka fara gudanar da al'amuransu a filin, yana mai cewa za a ci gaba da gudanar da ayyuka a filin kamar yadda aka saba gabanin rufe shi.
A watan Disamba na shekarar 2013 ne dai jami'an tsaron kasar suka bayar da umarnin rufe filin jirgin sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a sansanin sojin sama da ke birnin na Maiduguri.