An bukaci zababben Gwamnan jihar Filato, Barista Simon Bako Lalon ya sake gine babbar kasuwar Jos da ta kone, don bunkasa harkar kasuwanci da na tattalin arzikin jihar.
Da yake magana a kan bukukuwan ranar dimukurdiya, daya daga cikin ’yan kasuwar da ke kasuwanci a babbar kasuwar da ta kone, Alhaji Abdullahi Abdurrahaman mai magani ’yan, kwalli Jos, ya ce konewar kasuwar ta durkusar da harkokin kasuwancin jihar, wanda a sanadiyyar haka ya ya yawancin ’yan kasuwa barin jihar.
Alhaji Abdullahi ya kuma zargi Tsohon Gwamnan jihar, Jonah Jang game da kuntata wa jama’a a cikin shekaru Takwas din da ya’yi yana mulkin jihar. Ya ce, Gwamanan ya yi amfani da mukaminsa ya sanya dokokin da suka haramta wa kananan ’yan kasuwa yin kasuwanci a gefen kasuwar, da kuma hana dimbin matasan da ba su da aiki yin sana’ar haya da Babur. Ya ce, wannan ya haifar da wahalhalu ga mutanen da ke zaune a ciki da wajen babban birnin jihar.
Saboda haka sai ya roki sabon Gwamanan da ya hanzarta gina wannan kasuwa don saukake wa dimbin ’yan kasuwar da suke jihar gudanar da harkokinsu na saye da sayarwa. Ya ce kafin kasuwar ta kone, ’yan kasuwa daga jihohin Arewa maso Gabashin kasar nan, duk a Jos suke zuwa su sayi kayayyakin da za su kai jihohinsu su sayar. Amma tun da kasuwar ta kone, harkokin kasuwanci suka gurgunce a jihar.
A karshe ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Simon Bako Lalon da sauran shugabannin da suka dauki rantsuwar kama aiki murna, tare da yin fatan Allah ya ba su basira da kwarin gwiwar yi ma al’ummar kasar nan aiki.